Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Sojojin runduna ta 6 na Nijeriya sun tarwatsa wasu haramtattun wuraren tace mai tare da kama wasu mutane 50 da ake zargin ɓarayin mai ne a yankin Neja Delta, tare da mayar da hankali sosai kan jihar Ribas.
Ayyukan, wanda aka gudanar tsakanin 30 ga watan Yuni zuwa 13 ga Yuli, 2025, sun kuma kai ga ƙwace sama da lita 25,000 na kayayyakin man fetur da aka sace tare da gano wasu haramtattun wuraren hada-hadar mai da aka tsara don lalata bututun mai.
Muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar soji ta 6 ta sojojin Nijeriya Laftanar Kanar Danjuma Jonah ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin.
A jihar Ribas, sojoji sun ci gaba da daƙile yunƙurin sake kafa sabbin haramtattun wuraren hada-hadar tace mai, musamman a bakin kogin Imo. An wargaza wuraren tace mai bisa ƙa’ida ba a kusa da Obuzor da Ozaa West a Ukwa West da Ogba/Egbema/Ndoni na jihohin Abia da Ribas, da dai sauran su.
Sojojin sun kuma lalata ganga guda 35, da na’urar karɓan mai guda 14, da manyan na’urorin sanyaya tankin maibguda uku, tare da ƙwato sama da lita 6,000 na ɗanyen mai.
A Obiafor da ke ƙaramar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni, an lalata wani haramtaccen wurin tace mai.
An karɓe sarrafa ramukan da aka cika da lita 3,000 na Man Fetur, Lita 2,000 na Kalanzir, da lita 1,000 na ɗanyen mai.
Bugu da ƙari, an kama wani tafki mai ɗauke da sinadarai sama da lita 3,000 da ake amfani da su wajen tace mai, da ganguna 14 na ƙarfe 14, da buhu biyar ɗauke da sama da lita 250 na kayan tace kalanzir da dizal.
Irin wannan ayyuka da aka yi a dajin Okarki, a ƙaramar hukumar Ahoada ta Yamma, ya kai ga tarwatsa wasu wuraren ajiyar mai ba bisa ƙa’ida ba.
A jihar Delta, sojoji sun tare wani jirgin ruwa mai gudu ɗaya da wani kwale-kwalen katako na cikin gida a mashigin ruwa na Jeddo a ƙaramar hukumar Warri ta Kudu.
Jiragen ruwan na ɗauke da buhu 86 cike da sama da lita 1,720 na kayayyakin sata.
A unguwar Obiaruku da ke ƙaramar hukumar Ukwuani, sojojin sun bankaɗo jarkoki 24 na lita 25 kowannen su da dizal da aka tace ba bisa ƙa’ida ba. An kama wani kwale-kwalen katako cike da kayayyakin man fetur na sata a Ugbokodo Creek, ƙaramar hukumar Warri ta Kudu.
A jihar Bayelsa, sojoji sun tsananta aikin sa ido tare da kama wata babbar mota da wata silinda mai nauyin kilogiram 70 da ake kyautata zaton an yi ta fasa bututun mai a Ikarama a ƙaramar hukumar Yenagoa.
A unguwar Angiama da ke kudancin ƙaramar hukumar Ijaw, an samu nasarar ƙwato litar kayayyakin sata da dama, kuma an kama waɗanda ake zargin.
Har ila yau, a jihar Akwa Ibom, wani samame da aka kai a wani ɗakin ajiyar kaya a ƙaramar hukumar Ukanafun, ya kai ga gano wasu jarkoki 15 cike da tataccen dizal ba bisa ƙa’ida ba.
Danjuma ya ƙara tabbatar da cewa dakarun da ke ƙarƙashin runduna ta 6 za su ci gaba da mamaye wuraren da ake aiki da su – a kan hanyoyin ƙasa da na ruwa – don hana ɓarayin mai da sauran masu aikata laifuka ‘yancin gudanar da ayyukansu.
Danjuma ya bayyana cewa, ayyukan da ake ci gaba da yi na nuni da yadda rundunar ta ɗauki nauyin kare kadarorin mai na Nijeriya da kuma dawo da yankin Neja Delta cikin hayyacin ta.
