Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin Aasa Ta’annati (EFCC) ta hannun Sashinta na musamman da ke yaƙi da safarar kuɗaɗe ta rufe otel da gidaje na Hampton Hilton da ke Kaduna saboda saɓawa dokar haramta badaƙalar kuɗaɗe.
A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, shugaban sashen yaɗa labarai da yada labarai na EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan badaƙalar da otel ɗin ya yi, wanda aka gano a yayin tantancewar SCUML.
Ya ce, tantancewar farko da aka gudanar a ranar 4 ga watan Yunin 2024, ta gano wasu ayyuka da suka saɓa wa doka, lamarin da ya sa aka sanya rufe otel ɗin.
Oyewale, ya ce bin diddigin a ranar 13 ga watan Yuni, 2025, ya gano cewa otel ɗin ya ƙara karya wasu dokoki.
Ya ce, “SCUML shiyyar Kaduna na Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati, EFCC, ta rufe otel da gidajen Hampton Hilton a Kaduna, bisa rashin bin Dokar Halasta Kuɗi na 2022 da ‘Anti-Money Laundering and Combating the Finance of Terrorism’ (AML/CFT).
“An gano cewa otel ɗin ya aikata laifuka da dama a binciken farko da aka gudanar a kansa, a ranar 4 ga Yuni, 2024, wanda ya kai SCUML ta santa masa takunkumi.”
Saboda haka, ya ce SCUML ya ci tarar miliyan N2.3, tare da wa’adin kwanaki bakwai don biyan kuɗi tare da cikakken bin ƙa’idojin da suka dace.
