Bayan shekaru 22 Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan fanshon tsofaffin ma’aikatan Nigeria Airways

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan fansho ga tsofaffin ma’aikatan kamfanin jiragen sama na Nigeria Airways, bayan kusan shekaru 22 suna jiran haƙƙoƙinsu.

Wata sanarwa da hukumar wayar da kan jama’a ta ƙasa (NOA) ta wallafa a shafinta na X ranar Talata, ta tabbatar da cewa ma’aikatar sufurin jiragen sama ta ƙasa ta tabbatar da fara fitar da kuɗaɗen nan ba da jimawa ba, tare da alƙawarin gudanar da aikin cikin gaskiya da adalci.

“Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan fansho da aka daɗe ana jira ga tsofaffin ma’aikatan harkar jiragen sama, wanda zai kawo sauƙi ga dubban mutanen da suka yi aiki a wannan fanni. Wannan mataki na zuwa ne bayan dogon lokaci ana fafutukar ganin an biya su haƙƙoƙinsu, musamman ma’aikatan tsohon kamfanin Nigeria Airways,” in ji sanarwar.

Kamfanin Nigeria Airways, wanda Gwamnatin Tarayya ce ta mallaka gaba ɗaya, ya fara aiki tun shekarar 1958 kafin a dakatar da shi a 2003 saboda matsalolin cin hanci, rashin tsari da kuma basussuka masu yawa. Bayan rusa kamfanin, fiye da tsofaffin ma’aikata 6,000 ne suka kasance ba su karɓi cikakken fansho ko gratuti ɗin su ba, lamarin da ya sa aka shafe shekaru fiye da 20 ana neman adalci.

A shekarar 2018, ƙungiyoyin ma’aikatan jiragen sama kamar NUATE, ATSSSAN, da NAAPE sun yi barazanar rufe sararin samaniyar Najeriya idan gwamnati ba ta biya Naira biliyan 45 da ake bin ta ba. Hakanan, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da biyan Naira biliyan 22 a matsayin kaso na farko. Wasu daga cikin tsofaffin ma’aikatan sun mutu ba tare da sun karɓi haƙƙoƙinsu ba.

By ukarofi