‘Yan sandan Yobe sun yi ram da matar da ake zargi da kashe mijinta

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Damaturu

Rundunar ‘yan- sandan Jihar Yobe ta kama wata mata, mai kimanin shekaru 35 da haihuwa, Hadiza Mamuda, dake zaune a ƙauyen Garin Abba a ƙaramar hukumar Fika, bisa zargin kashe mijinta, biyo bayan saɓanin da ya kaure a tsakanin su, wanda ya samo asali kan abinci.

A cikin wata sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan-sanda a Jihar Yobe (PPRO), SP Dungus Abdulkarim ya fitar, ya bayyana cewa wadda ake zargin ta buga wa mijinta da itace, wanda hakan ya janyo munanan raunuka da suka yi sanadiyyar mutuwarsa.

Marigayin, mai mata biyu da ‘ya’ya biyar, sun wayi gari cikin alhini da baƙin cikin rasa shi, ciki kuwa har ita wadda ake zargin.

Yayin da ofishin yan-sanda yankin Fika ce ke jagoranci bincike kan lamarin, haka zalika kuma ta tabbatar da cewa za a gurfanar da wadda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

A lokacin da yake magana dangane da wannan al’amarin, kwamishinan ‘yan- sandan jihar, CP Emmanuel Ado, ya bayyana kaɗuwarsa kan wannan aika-aika, inda ya jaddada buƙatar haɗin gwiwar al’umma da shugabannin addini wajen kawo gyara ta hanyar sulhu a tsakanin al’umma don kaucewa afkuwar irin waɗannan ayyukan assha.

Ya kuma buƙaci shugabannin addini da na al’umma da su ƙara wayar da kan jama’a game da haɗurran cin zarafin juna a tsakanin ma’aurata, tare da jaddada muhimmancin warware saɓani cikin lumana.

Rundunar ta kuma sake jaddada ƙudirin ta na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar.

By ukarofi