Yadda uwa ta kashe ’ya’yan cikinta biyu saboda ƙuncin rayuwa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Ana zargin wata uwa a jihar Enugu da kashe ’ya’yanta biyu saboda tsananin ƙuncin rayuwa.

Lamarin ya faru a unguwar Trans Ekulu da ke yankin birnin na Enugu.

An ga gawarwakin yara biyu a gidan lokacin da jami’an tsaro suka shiga ciki, lamarin da ya tayar da hankulan jama’ar unguwar.

Yaran da ake zargin uwar tasu da kashewa sun haɗa da yarinya mai suna Esther Arinze mai shekara huɗu da haihuwa da kuma ƙaninta mai suna Chibusoma.

Ana zargin an yi amfani da makami mai kaifin gaske wajen ji wa yaran raunuka a jikunansu kafin su rasu.

Majiyar labarinmu da rundunar ’yan sandan yankin Trans Ekulu sun amsa kiran gaggawar ne daga unguwar aka shaida musu faruwar lamarin inda su kuma ba su yi ƙasa a gwiwa ba suka rankaya zuwa gidan inda suka iske gawarwakin yara jina-jina.

Daga bisani dai ’yan sanda sun kwashe gawarwakin yaran zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar Enugu, inda likitoci suka tabbatar da mutuwar su.

By ukarofi