Daga DAUDA USMAN a Legas
An bayyana cewa rasuwar tsohon shugaban ƙasar Nijeriya Marigayi Janaral Muhammadu Buhari bayan kwashe watanni a shirin da biyar da sauka kan karagar mulkin kasar nan, ta girgiza al’ummar Nijeriya dama na ƙasashen duniya baki ɗaya.
Sa’idu Abdullahi Alakwa Mabera, ɗan asalin jihar Sakkwato ta Kudu mazaunin Legas dake gudanar da harkokin kasuwancin tattasai a kasuwar Mile 12 Intanashinal maket a birnin Legas shine ya bayyana hakan a lokacin da yake yin tsokaci dangane da rasuwar marigayin, inda Sa’idu Abdullahi Alakwa Mabera Sakkwato ta Kudu ya cigaba da cewa haƙiƙa Nijeriya ta yi gaggarumin rashin gwarzon ɗan siyasa mai kishin ƙasar nan tare da al’ummar cikinta baki ɗaya. Ya ce akan haka yake gabatar da saƙon ta’aziyyarsa ga shugaban ƙasar Nijeriya na wannan lokaci Bola Ahmed Tunubu da ‘yan uwan marigayin da iyalansa da sauran al’ummar Nijeriya dama na ƙasashen duniya baki ɗaya dangane da wannan babban rashin da aka yi na gwarzon ɗan siyasa Marigayi Janaral Muhammadu Buhari, da fatan Allah Ubangiji ya jiƙansa da rahama ya gafarta masa kurakuransa ya kuma sanya aljanna ce makomarsa da shi da sauran Musulmin da suka rigamu gidan gaskiya.
A cewarsa marigayi tsohon shugaban ƙasar ta Nijeriya Janaral Buhari ya bada gudummawarsa ƙwarai da gaske a lokacin da yake kan karagar mulkin shugabancin ƙasar nan wajen riƙewa Nijeriya ‘yanci tare da kawo ayyukan cigabanta gaba ɗaya ya ce kadan daga cikin irin cigaban da ya kawo wa Nijeriya a lokacin da yana kan karagar mulkin shugabancin ƙasar nan akwai yunƙurin da ya yi na bunƙasa harkokin tattalin arzikin ƙasar nan wanda suka haɗa da noma kasuwanci tsaro da kiwon lafiya da bunƙasa harkokin ilimin zamani da sauransu.
Haka zalika Sa’idu Abdullahi Alakwa Mabera Sakkwato ta Kudu ya cigaba da nuna gamsuwarsa ga jagorancin babban shugaban kasuwar Mile 12 intanashinal market Alhaji Shehu Usman Jibirin samfam sardaunan Egbaland Abeokuta ta jihar ogun bisa ga ƙoƙarinsa na haɗa kawunan ‘yan kasuwar da sauran ƙabilu mazauna Legas domin cigaba da samun zaman lafiya a tsakanin su bakiɗaya.
Sannan ya cigaba da jinjina wa shugaban ɓangaren tattasai Alhaji Aminu Musa Kiru dangane da ƙoƙarin da yake yi na bunƙasa harkokin kasuwancin tattasai a Legas da kewayenta gabaɗaya haka kuma ya cigaba da jawo hankulan matasa da sauran ‘yan kasuwar da su cigaba da samar da zaman lafiya a kowanne lokaci.
