Daga RABIU SANUSI a Kano
Majalisar Dinkin Duniya ta ƙudiri aniyar tallafawa gwamnatin Kano a ɓangarori da dama domin dacewa da muradun Majalisar ɗinkin Duniya masu ɗorewa na 2030.
Mataimakiyar sakataren Majalisar ɗinkin Duniya Hajiya Amina Muhammad ce ta bayyana hakan a wata ziyara ta musamman da ta kawo jihar Kano kuma ta gana da gwamna Abba Kabir Yusuf.
A yayin ziyarar Hajiya Amina Muhammad ta yaba da ƙoƙarin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a bisa sauye-sauyen da ya samar a jihar.
Ta kuma shaida cewa Majalisar ɗinkin Duniya za ta yi aiki da jihohin Arewacin Nijeriya domin tabbatar da ɗorewar muradun majalisar na shekarar 2030.
“Kano na da mahimmaci matuka ga wannan shiri na majalisar,kuma majalisar zata duba wasu matsaloli da suke damun Arewa musamman a Kano.”
“Muna sane da cewa jihaKano nada matasa masu dinbin yawa da kuma nuna karewa a ƙirƙire-ƙirkire, sannan majalisar za ta duba ɓangarori da suka haɗa da ilimi da lafiya da noma da sauransu.
Hajiya Amina ta ce, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma nuna gamsuwarsa akan wannan ƙudiri na majalisar ta ɗinkin Duniya.
Wakilinmu ya rawaito a shekarar 2015, ƙasashen duniya da ke cikin Majalisar ɗinkin Duniya ciki har da Nijeriya suka amince da manufofi 17 domin kawo ci gaba mai ɗorewa zuwa shekara ta 2030.
Amina Muhammad ta kuma ce ta zo Nijeriya ne domin ta’aziyyar marigayi tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wanda ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata a London.
Daga nan gwamna Yusuf ya gode wa mataimakiyar Shugaban majalisar ta ɗinkin duniya tare da tabbatar mata da cewa gwamnatinsa a shirye take domin yin aiki tare.
Gwamna ya kuma matukar farin cikin sa bisa wannan ziyara da ya bayyana a matsayin girmamawa matakin farko.
Haka zalika duka cewa Hajiya Amina Muhammad ta faɗi buƙatar tallafawa jihar shi, ya ƙara miƙa ƙoƙon bararsu wajen a ƙara samar da hanyoyin da matasa da al’ummar Jihar za su samu madogara.
