Yadda EFCC ta kama ɗaliban Jami’ar Bayero 25 bisa zargin zamba ta intanet

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, EFCC, ta kama wasu mutane 25 da ake zargi da damfara ta yanar gizo a wani samame da ta kai a Kano.

Kakakin ta, Dele Oyewale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Laraba.

Mista Oyewale ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a ranar Litinin, daura da Jami’ar Bayero Kano, BUK, New Site, Kano.

A cewarsa, kama su ya biyo bayan bayanan sirri ne da ake zargi da hannu a ayyukan damfara ta yanar gizo.

“Dukkan waɗanda aka kama an tabbatar da cewa ɗaliban BUK ne masu karatun digiri na farko.

“Abubuwan da aka gano a yayin aikin sun haɗa da, wayoyin hannu, kwamfutar tafi-da-gidanka, na’urorin sadarwa na intanet da kuma mota ƙirar Honda Accord guda ɗaya,” inji shi.

Ya ce an kama su ne biyo bayan sa ido da aka yi na tsawon makonni ana alaƙanta su da laifin damfarar intanet, satar bayanan sirri, da badaƙalar kuɗi.

“Za a gurfanar da waɗanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike,” inji shi.

By ukarofi