Majalisar Dinkin Duniya za ta dakatar da tallafin abinci a Arewa maso Gabashin Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shirin Abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ya bayyana cewa daga ƙarshen watan Yuli, zai dakatar da tallafin gaggawa na abinci da kiwon lafiya ga mutum miliyan 1.3 a Arewa maso gabashin Nijeriya saboda ƙarancin kuɗi.

Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da tashe-tashen hankula ke ƙaruwa, kuma yunwa na kai matsayi mafi muni a tarihin aasar.

WFP ya ce, kayan abinci da na kiwon lafiya sun ƙare gaba ɗaya, kuma rabon da ake yi yanzu shi ne na ƙarshe.

Idan ba a samu tallafi cikin gaggawa ba, mutane da dama za su fuskanci yunwa, gudun hijira ko kuma shiga hannun ‘yan tada ƙayar baya.

Daraktan WFP a Nijeriya, Daɓid Steɓenson, ya ce kusan mutum miliyan 31 ke fama da matsanancin yunwa a ƙasar wanda shi ne mafi yawa a tarihi.

“Yara ƙanana za su fi shan wahala, domin fiye da asibitoci 150 a Borno da Yobe da ke kula da yara ƙasa da shekaru biyu za su rufe,” inji daraktan.

WFP na buƙatar dala miliyan 130 domin cigaba da ayyukanta har zuwa ƙarshen shekarar 2025.

Rikicin da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi ke ci gaba da yi na ci gaba da haifar da tarwatsewar jama’a, inda mutane miliyan 2.3 a yankin tafkin Chadi tuni suka ƙauracewa gidajensu.

WFP ya yi gargaɗin cewa yanzu ana iya tilastawa da yawa yin hijira don neman abinci da tsaro ko kuma komawa ga kungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a matsayin mafita ta ƙarshe.

“Taimakon abinci na iya hana waɗannan sakamakon sau da yawa,” inji Steɓenson. “Yana ba mu damar ciyar da iyalai, sake gina abubuwan rayuwa, da tallafawa murmurewa na dogon lokaci.”

WFP ya ce ta yi nasarar kaiwa ga mutane miliyan 1.3 a farkon rabin shekarar 2025, kuma tana shirin tallafawa ƙarin 720,000 a rabin na biyu na shekara.

Sai dai a halin yanzu yunƙurin ya ci tura sakamakon giɓin kuɗaɗe na dala miliyan 130, lamarin da ke barazanar dakatar da muhimman shirye-shirye.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “WFP na da ƙarfin da za ta iya ɗaukar matakan da take ɗauka na jinƙai,” inji sanarwar, “amma giɓin tallafin da ake samu yanzu yana gurgunta ayyukanmu.”

A halin yanzu ƙungiyar na yin kira ga ƙasashen duniya da su taimaka wajen daƙile durƙushewar ayyukan jinƙai a yankin arewa maso gabashin Nijeriya, da kuma kare rayukan miliyoyin mutane da ke fuskantar barazanar yunwa da tamowa.

By ukarofi