APC na daf da samun kashi biyu bisa uku a Majalisar Dattawa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Adadin sanatocin jam’iyyar APC mai mulki ya kusan haura 73 wanda shi ne kashi 2 cikin 3 na dukka sanatoci 109 da ake da su a Majalisar Dattawa.

Jam’iyyar wadda ta samu zaɓaɓɓun sanatoci 50 a farkon zaman majalisar dattawa ta 10 a watan Yunin 2023, ta haura zuwa 68 a yanzu, saboda ficewar sanatoci daga PDP, Labour Party da NNPP zuwa jam’iyyarta, na baya-bayan nan daga cikin waɗanda suka sauya sheƙa sun haɗa da Sanata Olubiyi Fadami Fayose da kuma Sanata Olubiyi Fagge.

Sanatocin da suka sauya sheƙar zuwa APC daga PDP sun haɗa da Francis Fadahunsi daga Osun ta Gabas da Oluwale Olubiyi daga Tsakiyar Osun da Aniekan Bassey na mazaɓar arewa maso gabashin jihar Akwa Ibom da kuma Samson Ekong daga Kudancin jihar Akwa Ibom. 

Kujeru 68 kuma na yankin Nasarawa ta Yamma ne wanda Sanata Aliyu Wadada Ahmed ke zaune a watan Mayun bana, ya shaida wa manema labarai cewa zai sauya sheƙa daga jam’iyyar SDP zuwa APC domin nuna adawa da Mallam Nasir El-Rufai wanda ya sauya sheƙa daga APC zuwa jam’iyyar kafin ya koma ADC tare da ‘yan siyasa a sassan jam’iyyar a farkon wannan watan.

Duk waɗannan sun kasance a gefe guda biyu da ba kowa a cikin kujerun Anambra ta Kudu da Edo ta tsakiya da za a cike ta hanyar zaɓe a wata mai zuwa.

Kujeru biyu da ba kowa a yanzu dai sanatoci ne a ƙarƙashin jam’iyyar APC a tsakanin marigayi Sanata Ifeanyi Ubah (Anambra ta Kudu) da kuma Monday Okpebolo a yanzu gwamnan jihar Edo.

Sakamakon haka, yayin da adadin Sanatoci a jam’iyyar APC ke ƙaruwa zuwa kashi 2/3, waɗanda ke kan dandamali na ƙananan jam’iyyu, su na raguwa sosai.

Jadawalin yawan ’yan majalisar dattawan da jam’iyyu ke da su a yanzu: APC 70, PDP 28, Labour Party 5, NNPP 1, SDP 2, APGA 1

PDP wadda ke da Sanatoci 45 a shekarar 2023, ta ragu zuwa 30, kuma za ta samu raguwa a cikin makon wata da sanatocin Akwa Ibom, suka amince da sauya sheƙa a zauren majalisar.

Haka kuma jam’iyyar Labour wadda ta ke da Sanatoci 8 a farkon zaman majalisar dattawa ta 10 a watan Yunin 2023, yanzu tana da Sanatoci biyar kamar yadda NNPP ke da biyu tun farko, yanzu ta koma ɗaya.

A halin yanzu, yayin da Sanata Wadada ta fice daga jam’iyyar SDP zuwa APC, jam’iyyar har yanzu tana riƙe da kujeru biyu a majalisar dattawa kamar yadda jam’iyyar APGA ke riƙe da kujera ɗaya (Abia ta Kudu) a majalisar dattawa, har zuwa lokacin da Sanata Enyinnaya Abaribe ya fice daga ita zuwa ADC.

Jadawalin yawan sanatoci ga jam’iyyu a Yunin 2023: APC 59, PDP 36, Labour Party 8, SDP 2, NNPP 2, APGA 1, YPP 1.

Majalisar Wakilai kamar takwararta da dattijai, a ranar Larabar da ta gabata ’yan majalisar uku ne suka sanar da ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa ta APC mai mulki.

’Yan majalisar wakilan da suka sauya sheƙar su ne: Hon. Ajilesoro Taofeek Abimbola daga jihar Osun, Hon. Omirin Olusanya daga jihar Osun, Hon. Marcus Onobu daga jihar Edo.

Dangane da dalilansu na ficewa daga PDP, shugaban majalisar wakilan, Tajuddeen Abbas yayin da yake karanta wasiƙunsu ga zauren majalisar ya ce sun bar PDP saboda rikicin cikin gida da rashin tabbas da suka baibaye jam’iyyar.

Jadawalin ‘yan majalisar da suka koma APC kafin yanzu: Hon, Idris Sulaiman Abubakar daga jihar Kogi – ADC zuwa APC, Hon. Chris Nkwonta daga Abia -PDP zuwa APC, Hon. Sulaiman Abubakar daga Zamfara – PDP zuwa APC, Hon. Chinedu Okere daga Imo, Hon. Mathew Donatus daga Kaduna, Hon Bassey Akiba daga jihar Ribas, Hon. Esosa Iyawe daga jihar Edo, Alfred Ajang daga Filato, Hon. Amos Magaji daga Kaduna, Hon. Garba Koko daga Kebbi

’Yan majalisar wakilai shida daga jihar Delta, Hon Kabiru Usman daga Kano – NNPP zuwa APC, Hon Abdullahi Sani – NNPP zuwa APC 

Jadawalin yawan kujeru ga jam’iyyu a majalisar wakilai a 2023: APC 162, PDP 102, LP 34, NNPP 18, APGA 4, ADC 2, SDP 2, YPP 1

A yanzu haka ƙididdiga ta nuna cewa jam’iyyar APC mai mulki na da ’yan majalisar wakilai 210, inda ta samu ƙarin ’yan majalisa 48 sakamakon sauya sheƙa daga jam’iyyun hamayya musamman babbar jam’iyyar hamayya ta PDP.

Kuma hakan na nuni da cewa akwai yiwuwar jam’iyyar APC ka iya samu gagarumin rinjaye na 240 na baki ɗaya ‘yan majalisar wakilan 360, wani abun da zai bai wa jam’iyyar damar amince wa da buƙatun ɓangaren zartarwa ba tare da samun cikas ba.

By ukarofi