Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Babban Jojin Jihar Katsina, mai Shari’a Musa Ɗanladi Abubakar, ya buƙaci Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina da ta samar da doka da za ta tanadi wani kaso na musamman a cikin kasafin kuɗin kowace shekara domin kula da makarantun koyar da ilimin addinin Musulunci a faɗin jihar.
Ya faɗi haka ne a yayin bikin walimar saukar Alƙur’ani mai girma da ɗaliban makarantar “Al-Ilham Islamic College” suka gudanar, makarantar da aka kafa bisa gudummawar dattijo kuma mai kishin addini, Alhaji Usman Sarki, a unguwar Ƙofar Guga cikin garin Katsina.
Mai Shari’a Musa Ɗanladi ya jaddada cewa ilimin addini na da matuƙar muhimmanci wajen gina tarbiyyar al’umma, saboda haka ya zama wajibi ga gwamnati ta tallafa wa irin waɗannan makarantu da kuɗi domin inganta su.
An kuma yaba wa dattijon Alhaji Usman Sarki bisa jajircewarsa wajen tallafa wa harkokin addini ta hanyar gina masallatai da makarantu na Islamiyya domin cigaban tarbiyyar al’umma.
Taron ya gudana a babban ɗakin taron hukumar ɗaukar ma’aikatan ƙananan hukumomi na Jihar Katsina, inda manyan baƙi suka halarta ciki har da fitattun malamai daga cikin jihar da wajenta. Cikin waɗanda suka halarta akwai Malam Yakubu Musa Hassan, Malam Aminu Yammawa, Shugaban hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, Dr. Aminu Usman Abu Ammar, da Malam Assaudu Sunnah.
Malaman sun gabatar da jawabai masu cike da nasiha da wa’azi ga mahalarta, inda suka jaddada muhimmancin karatun Alƙur’ani da ilimin addini gaba ɗaya. Haka kuma, sun jawo hankalin masu hannu da shuni da su bi sahun Alhaji Usman Sarki wajen saka jari a tarbiyyar al’umma.
Daga cikin manyan baƙi da suka halarci taron akwai Ɗan Majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Aliyu Abubakar Albaba, Alhaji Mannir Ayuba Sulluɓawa, Hon. Babangida Nasamu, Alhaji Lolo Dakare Ƙofar Guga, Alhaji Aminu Wali, Alhaji Ɗahiru Usman Sarki da Alhaji Ibrahim Teacher, tare da wasu fitattun ‘yan ƙasa.
A ƙarshe, an raba kyaututtuka ga ɗaliban da suka sauke Alƙur’ani, musamman waɗanda suka samu matsayi na ɗaya, na biyu da na uku, tare da girmamawa ga malamansu da kuma Alhaji Usman Sarki wanda shi ne ya assasa makarantar.
