Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Majalisar Dokoki ta Jihar Zamfara ta tattauna tare da amincewa da a dakatar da shugaban hukumar ZAROTA.
Sanarwar na ƙunshe ne a wata takarda da sakataren hulɗa da ƴan jaridu Bello Madaro ya rattaɓa wa hannu a yau Laraba.
Sanarwar ta bayyana cewar, Majalisar Dokoki ta Jihar Zamfara a zamanta na yau Laraba ta tattauna tare da kira ga gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya dakatar da shugaban hukumar ZAROTA na jihar MB Musa bisa zargin rub da ciki da kuɗaɗen hukumar.
Hakan ya biyo bayan rahoton da kwamitin kula da ɗa”a na majalisar ƙarƙashin jagorancin Hon Rilwanu Marafa Anka ya gabatar bayan gudanar da bincike a kan tuhumar da ake yiwa shugaban ZAROTA na rub da ciki da fiye da Naira Miliyan 11 kuɗaɗen hukumar ZAROTA.
A lokacin gabatar da rahoton Hon Rilwanu Marafa Anka yace binciken kwamitin ya gano wannan badakalar ne bayan bin diddigin yadda kuɗaɗen suka shigo da kuma yadda suka zurare ba kan ƙa’ida ba.
Daga nan yace ya zama wajibi a hukunta wanda lamarin ya shafa ta hanyar ɗaukar matakin dakatar dashi nan take kafin samar da kamalallen rahoto.
A gudunmawar da suka bayar waɗansu daga cikin mambobin majalisar dokoki ta Jihar Zamfara sun jinjinawa kwamitin a kan wannan ƙoƙari tare da nuna goyon bayansu akan dakatar da shugaban hukumar ta ZAROTA har sai an kammala bincike.
Daga bisani bayan amincewar dukkanin mambobin majalisar dokokin, sai na’ibin shugaban majalisar Hon Adamu Aliyu Gummi wanda ya jagoranci zaman na yau ya sanar cewa majalisar ta tattauna tare da amincewa da rahoton kwamitin kula da ɗa’a na majalisar, da kuma kira ga gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya dakatar da shugaban hukumar ZAROTA na wucin gadi kafin gudanar da cikakken bincike.
