
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ƙoƙarinsu na magance matsalolin ayyukan ta’addanci, jami’an soji sun yi nasarar daƙile shirin mayaƙan Boko Haram na dasa waɗansu ababen fashewa a wata gada dake hanyar Dikwa zuwa Marte a Jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an sun yi galaba akan mayaƙan ne a lokacin da suka shigar dasa boma-bomai da nufin katse hanyoyin zirga-zirgan jami’an gami da raba ƙauyuka, lamarin da ya sa aka yi ba-takashi a tsakanin ɓangarorin biyu da fatattakar ƴan ta’addan.
Sojojin sun yi nasarar ƙwato manyan sinadaran ababen fashewa guda biyu da wasu muggan makamai a wajen da abin ya faru.
An gudanar da atisayen ne a ƙarƙashin dakarun Atisayen HAƊIN KAI, wanda aka samar da shi da nufin daƙile ayyukan ƴan ta’adda da a yankunan Tafkin Chadi, Dajin Sambisa da Duwatsun Mandara.
Da ya ke ganawa da manema labarai ta wayar tarho, Kwamandan rukunin dakarun, Manjo Janar Abdulsallam Abubakar ya yaba wa jami’an bisa hoɓɓasa da suka da jarumta da suka nuna game da lamarin.
Ya kuma ce, jami’an a ƴan makonnin nan suna kutsawa wuraren da ƴan ta’adda suka fake tare da tarwatsa su.
A yayin daƙile shirin ne aka halaka guda tara daga cikin mayaƙan a Ƙananan Hukumomin Bama, Gwoza da Konduga.
Haka kuma sojojin sun ƙwato makamai da suka haɗa da bindigu ƙirar AK-47 da masu jigida da alburusai da dama, lamarin da ya haddasa tarwatsewarsu.
