Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Amincewa da dokar ya biyo bayan yima dokar karatu na uku, a zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin kakakin ta Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura.
Majalisar ta fara karanta ƙudirin ta yin dokar karatu na farko dana biyu a zaman majalisar, wanda majalisar ta ɗauki tsawon wuni tana tafka mahawara kan dokar, kafin daga bisani ta amince da ita.
Dokar wadda ɓangaren zartarwa na jihar ya buƙaci majalisar tayi ta shafi sa ke fasalin harkokin masarautar Katsina da kuma sa ke fasalin majalisar sarakuna na Jihar Katsina.
A kwanan baya ne dai wata ƙungiya ta kai wa majalisar dokokin Katsina takardar buƙatar ƙirƙiro da ƙarin masarautu uku daga cikin masarautar Katsina
Duk a zaman majalisar, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Dutsinma Hon. Abubakar Muhammed Khamis ya gabatar da ƙudirin ƙara kai ɗaukin gaggawa ga al’ummar ƙaramar hukumar Dutsinma a kan matsalolin tsaro da yankin yake fama da shi.
Kazalika ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ɗandume ya gabatar da ƙudirin buƙatar gina ƙaramin filin wasa a ƙaramar hukumar Ɗandume domin taimaka ma harkokin matasa da wasanni a yankin.
Bayan gabatar da ƙudirorin, daga ƙarshe majalisar ta amince, inda Kakakin majalisar ya umurci akawun majalisar da ya tura ma ɓangaren zartarwa domin ɗaukar matakin da ya dace.
Duk da babu wani bayani dangane da buƙatar na gwamnatin Katsina kan sake fasalin masarautar Katsina, wannan mataki ba zai rasa nasaba da takun saƙa tsakanin masarautar Katsina da Gwamna Dikko Raɗɗa.
