Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Honarabul Abdullahi Hassan Tsamiya ɗaya daga cikin manyan masu bai wa gwamnan Kebbi shawara kuma jigo a siyasar ƙaramar hukumar mulki ta Argungu da ke jihar Kebbi ya ajiye muƙamin sa tare da sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta ADC.
Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun sa a ranar Lahadin da ta gabata da aka raba wa manema labarai.
Takardar ta bayyana cewa Honarabul Abdullahi Hassan ya ajiye mukamin sa ne bayan wani nazari da ya yi a kan rashin adalci da rashin mutuntawa da kyautatawa zuwa ga wadanda suka bayarda gudummawa wajen kafa wannan gwamanti a shekarar 2023.
Takardar ta ƙara da cewa ya bi duk hanyar da ya ke ganin zai iya bi don ya cigaba da taimakawa mutanen sa amma hakan ya faskara saboda haka ya yanke shawarar ficewa daga Jam’iyyar APC tare da shiga Jam’iyyar ADC inda ya ke sa ran shawarwarin sa da gudummawar da zai bayar ba za su tafi a banza ba.
Takardar ta kuma bayyana cewa Honarabul Abdullahi Hassan yana alfahari da gudummawar da ya bayar wajen kafa gwamnatin APC.
Wannan dai shi ne mai baiwa gwamnan jihar Kebbi na biyu da suka ajiye mukamin su tare da barin Jam’iyyar APC zuwa ADC inda sati biyu da suka gabata shi ma tsohon danmajalisar Zartaswa da ya wakilci ƙaramar hukumar mulki ta Argungu Honarabul Nasiru Muhammed ɗan Umma ya sanar wa duniya cewa ya fice daga APC ya koma ADC.
