Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan Sufuri na ƙasa, Sa’idu Alkali, ya bayyana cewa aikin titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano zai kammala nan da shekarar 2026, inda ya bayyana cewa aikin wanda ya tsaya a kashi 15 cikin 100 kafin zuwan gwamnatin Tinubu, yanzu ya kai kashi 53 cikin 100.
Ya sanar da hakan ne yayin jawabinsa a taron tattaunawa tsakanin gwamnati da jama’a da Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation ta shirya a Kaduna.
Alkali ya ce yankin Arewa na daga cikin mafi yawan waɗanda ke cin moriyar ayyukan ci gaban ababen more rayuwa na gwamnatin Tinubu ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda.
Ya ƙara da cewa aikin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Maradi ya kai kashi 61 cikin 100, yayin da wasu sassa na aikin titin jirgin ƙasa daga Fatakwal zuwa Maiduguri ke ci gaba da gudana.
Ya ce aikin manyan hanyoyi kamar Sokkwato zuwa Badagry mai tsawon kilomita 1,068 wanda ya haɗa jihohi bakwai yana daga cikin manyan ayyuka da gwamnati ke aiwatarwa don bunƙasa haɗin kai da tattalin arzikin kasa. Hakazalika, an fara aikin gyaran layin jirgin ƙasa daga Legas zuwa Kano domin sauƙaƙa jigilar kaya.
A ɓangaren makamashi, Alkali ya bayyana cewa Hukumar Wutar Lantarki ta Karkara (REA) ta girka fiye da na’urorin hasken rana 1,100 da kuma gina ananan wurin samar da lantarki guda 32 a jihohin Arewa maso Gabas.
Ya ƙara da cewa an gina gidaje fiye da 3,000 a jihohin Arewa ƙarƙashin shirin Renewed Hope Cities, kuma ana shirin kafa sabbin tashoshin sufuri a kowane yanki na na ƙasar nan.
