Mashawarcin Gwamna Raɗɗa ya rasu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Allah ya yiwa Hon Nasidi Ɗanladi Garki rasuwa, kafin ya rasu yana riƙe da muƙamin mai ba gwamna Raɗɗa shawara kan cigaban al’umma.

Marigayi Nasidi ɗan asalin ƙaramar hukumar Ɓaure ya taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukumar Ɓaure har karo na biyu daga nan ya wuce majalisar wakilai nan ma har karo na biyu.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya ce ya kaɗu ƙwarai da samun labarin rasuwar Hon Nasidi.

A wata takardar sanarwa ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na gwamna Kabul Muhammad,gwamnan ya bayyana marigayi Nasidi a matsayin mutum mai haƙuri da tausayi da taimakon al’umma musamman a yankin da ya fito.

“Marigayi Nasidi Ɗanladi mutumin kirki wanda ko da yaushe yana tare da mutanen.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya miƙa ta’aziyar sa a madadin gwamnatin Jihar Katsina ga masarautar Daura da iyalan mamacin da addu’ar Allah masa rahama ya yafe masa kurakuransa.

By ukarofi