Daga USMAN KAROFI a Abuja
Shugaban ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Anas Mukthtar Bello Ɗanmaliki, ya bayyana aniyar ƙaramar hukumar na bin duk matakan da suka dace domin ganin an biya hakkokin mutanen da aikin titin jirgin ƙasa ya shafa a garin Tumfafi.
Ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi tawagar mutanen da abin ya shafa a ofishinsa, inda suka kai masa koke kan yadda gonakinsu da kadarorinsu suka shiga aikin ba tare da cikakken biyan diyya ba.
Alhaji Ɗanmaliki ya roƙi jama’ar da abin ya shafa da su kwantar da hankalinsu, yana mai tabbatar musu cewa ƙaramar hukumar ba za ta zura ido ba a tauye haƙƙoƙinsu. Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda matsalar ta hana wasu daga cikinsu gudanar da harkokin noma a gonakinsu.
A yayin zantawarsa da su, shugaban ƙaramar hukumar ya shawarce su da su ba da muhimmanci wajen sanya ‘ya’yansu a makaranta domin samun ingantaccen ilimi da makoma mai kyau.
Jagoran masu korafin, Malam Sagir Usman Tumfafi, ya bayyana cewa a wasu lokuta ana ba su diyya kadan fiye da ainihin kuɗin da gonakinsu ya dace a biya. Ya ce sun shafe tsawon shekara guda suna kai ƙara kotu kan batun, amma duk lokacin da suka shigar da takardar gargaɗi, sai a sake tura su gefe domin ci gaba da aikin.
“Gonar naira miliyan talatin an dauki naira dubu dari da ashirin aka ba mu. Wata gonar da ta kai kafa dari uku da hamsin ita ma haka aka yi. Wannan shi ne dalilin da ya sa muka garzaya hukumomi, domin kada rikici ya ɓarke,” in ji shi.
