Yanzu-yanzu: INEC na shirin bai wa fursunoni damar kaɗa kuri’a yayin zaɓuka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta sanar da shirinta na bai wa fursunoni damar kaɗa kuri’a a yayin zaɓuka a Nijeriya.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ya faɗi haka a yau Juma’a yayin karɓar baƙoncin Kwantirola Janar na Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali (NCoS), Sylvester Nwakuche a hedikwatar INEC da ke Abuja.

Ya hakaito hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na tabbatar da ƴancin fursunoni na su yi rajista da zaɓe, inda kuma tuni suka nemi NCoS ta fara shirin aiwatar da hakan duba da koken jam’iyyun siyasa game da lamarin.

Haka kuma, Farfesan ya ce akwai buƙatar majalisar dokoki ta bai wa al’amarin muhimmanci wajen ganin an fara barin mazauna gidajen yari kaɗa kuri’a a yaki6n gudanar da zaɓukan ƙasar kamar yadda dokar ƙasa ta bada dama.

Hakan ya biyo bayan ƙorafi da Nwakuche ya shigar wa INEC kan ta ba wa fursunoni ƴancin yin zaɓe.

Ya bayyana cewa, akwai aƙalla fursunoni 81,000 a gidajen yarin Nijeriya, waɗanda kaso 66 daga cikin suna jiran hukunci nedaga kotuna.

By Babaji