Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon shugaban PDP kuma ministan Buhari, Audu Ogbeh ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Ministan Noma da Raya Karkara, Cif Audu Ogbeh ya rasu bayan shafe shekaru 78 a duniya.

Marigayin ya rasu ne a yau Asabar 9 ga watan Agusta, 2025.

A wata sanarwa daga makusantansa, za a sanar da lokacin gudanar da jana’izarsa.

Sun bayyana godiyarsu ga abokai, abokan aiki da masu fatan alheri a yayin jimamin rashin.

Ogbeh shi ne shugaban jam’iyyar PDP daga shekarar 2001 zuwa 2005, sannan minista ne a zamanin mulkin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Haka kuma shi ne ministan sadarwa a zamanin mulkin marigayi tsohon shugaban ƙasa Shehu Shagari daga 1982 zuwa 1983.

Bugu da ƙari, ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin kakakin majalisar dokoki ta Benuwai a ƙarshen shekarun 70s.

By Babaji