
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mutane da dama sun rasu yayin da wasu suka jikkata bayan wata tanka maƙare da mai ta fashe a Jihar Kaduna.
Lamarin ya auku ne a safiyar yau Litinin kusa da makarantar Rochas Foundation School da ke babban titin Kaduna zuwa Kano a tsakanin Kwangila zuwa Ɗan Magaji dake yankin Zariya.
Mai sharhi kan lamuran daƙile ayyukan ta’addanci, Zagazola Makama, ya ce lamarin ya rutsa ne da wasu tankokin mai biyu da motocin Golf biyu da ke cike da fasinjoji.
Wani shaida ya ce, a iftila’in an ga fashewar wuta sau biyar tare da hayaƙi mai duhu.
Ya kuma ce, baki ɗaya mutanen da ke cikin motocin sun rasu a nan take sai wani direba ɗaya da ya tsira, wanda shi ma ya samu munanan ƙuna.
Tuni jami’an bada agajin gaggawa da na hukumomin tsaro suka garzaya wajen da abin ya faru.
