An ƙaddamar da Mr Steven Akwaden a matsayin sabon shugaban ICAN na bakwai reshen Lafiya

Spread the love

Daga JOHN WADA a Keffi

Wata ƙungiya da aka fi sani da “The Institute of Chartered Accountants of Nigeria” (ICAN) a turance, reshen Lafiya Jihar Nasarawa ta gudanar da wani babban taron naɗin sabon shugaban ƙungiyar, Mr. Akwaden Stephen Thomas, FCA, a matsayin shugaban ƙungiyar na bakwai, tare da ƙaddamar da wasu sabbin jagororin kwamitin gudanarwar ƙungiyar na shekarar 2025 da 2026.

Taron ya gudana ne a babban dakin taron jami’ar da ake Kira S.B. Mohammed Auditorium a turance inda aka samu halartar manyan mutane daga wurare daban-daban ciki har da tsohon mataimakin shugaban jami’ar, Prof. Suleiman Bala Mohammed da sauran su.

Da take jawabi a wajen taron, shugabar babban jami’ar ta Jihar Nasarawa, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman, wacce Farfesa Maikano Ari ya wakilta, ta godewa ICAN saboda naɗin Akwaden a matsayin sabon shugaba inda ta yaba wa Akwaden musamman ta ƙwarewar sa a fannin lissafin kuɗi, sannan ta taya shi murnar sabon muƙamin nasa.

Ta cigaba da bayyana cewa, “Na gode wa ICAN saboda tabbatar da imaninmu.

Stephen Thomas Akwaden mutum ne mai gaskiya, kyakkyawan hali, da mutunci.

A madadin jami’ar nan ta NSUK, za mu ci gaba da nuna masa goyon bayan mu da ICAN baki ɗaya, mu kuma muna tabbatar da cikakken haɗin gwiwa mai amfani don cigaban ƙungiyar, jami’ar nan da ma al’umma baki ɗaya.

Ina kuma yin Kira ga dukkan mambobin ƙungiyar su bashi cikakken goyon baya don bashi damar samun nasarori wa ƙungiyar.” Inji ta.

A nasa ɓangaren da yake jawabi bayan an ƙaddamar dashi a matsayin sabon shugaban ICAN ɗin reshin Lafiya, Mr. Thomas Steven Akwaden ya ce wannan lokaci ba wai kawai abin alfahari ne na kashin kansa ba, har ma wani alƙawari ne na hidima da kuma gane ƙoƙarin mambobin ICAN wajen inganta harkokin ƙungiyar.

Ya ce, “Jagorancin mu zai cigaba da mai da hankali ne wajen ɗaukar nauyin inganta sana’oi da faɗaɗa tasiri.

Manufarmu za ta dogara ne akan ginshiƙai guda biyar: ƙara yawan ɗalibai da matasa, shirye-shiryen CPD masu dacewa, ayyukan al’umma, haɗin gwiwa na ilimi, da ƙarfafa tsarin mulki da gado.”

Ya kuma sanar da cewa zai ɗauki nauyin kusan ɗalibai 50 masu zuwa da suka kammala karatun digiri a jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi waɗanda suka cancanci yin jarrabawar ICAN.

A cikin saƙonnin nishaɗi, tsohon mataimakin shugaban jami’ar, Prof. Suleiman Bala Mohammed, da Prof. G.A. Amuga, sun yaba wa Akwaden saboda gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa jami’ar inda suma sauran sabbin jagororin ƙungiyar aka ƙaddamar dasu daga bisani.

By ukarofi