Daga UMAR GARBA a Katsina
Haɗarin ya faru bayan da marigayin, Abdulsalami Yusuf Ƙanqara, mai shekaru 37, da matarsa, Malama Zainab, suka dawo daga ƙaramar hukumar Kurfi, inda suka ziyarci wasu ma’aurata domin jajanta musu ɓarin ciki da suka samu.
Ɗan uwan Abdulsalami, Aminu Yusuf Ƙanqara, ya ce wani babur ɗauke da mutane uku ne ya haddasa haɗarin bayan mai babur ɗin ya goya mutum biyu lamarin da ya sa babur ɗin yayi karo da motar su.
“Mutanen dake kan babur da kuma matar Abdulsalami sun mutu nan take, daga bisani Abdulsalami ya rasu bayan an kai shi asibiti,” in ji shi.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa direban babur ɗin dake ɗauke da fasinjoji biyu ya kutsa kai kan hanyar motar, lamarin da yayi sanadin mutuwar dukkan mutanen uku da ke kan babur ɗin nan take, a yayin da aka garzaya da sauran mutanen da ke cikin motar zuwa asibiti, inda daga baya Abdulsalami ya rasu sakamakon raunin da ya samu.
Masu jimamin haɗarin sun bayyana marigayi Abdulsalami a matsayin mutumin kirki, marigayin shi da matarsa sun yi aure watanni kaɗan da suka gabata.
