Rawar da Dakta Matawalle ke takawa wajen inganta harkoƙin tsaro a Nijeriya

Spread the love

Daga BASHIR ALIYU

Tun da aka naɗa shi a matsayin ƙaramin Ministan Tsaro a 2023, Dakta Bello Matawalle ya sake kawo sabon dabaru ta fannin tsaro, nazari da kuma ɗaukar matakan da suka jiɓi dasa tubalin ginin sashen tsaro na ƙasa. A lokacinsa an samu manyan nasarori a ɓangaren yaƙi da ta’addanci, zamanantar da rundunar soja, da kuma tabbatar da zaman lafiyar ƙasa, waɗanda ne suka sa ake kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan mutunen da suke bayar da muhimmiyar gudummawa wurin yaƙi da rashin tsaro.

A lokacin jagorancinsa ne Ma’aikatar Tsaro ta samu manya-manyan nasarori domin kawo zaman lafiya a ƙasa. Waɗannan nasarori su ne:

  1. Nasarori a kan ta’addanci da satan mutane

ɗaya daga cikin manyan nasarorin da Dakta Bello Matawalle ya samu shi ne ƙaimi da aka yi wurin yaƙi da ta’addanci, ta hanyar kyautata haɗin gwiwa da Sojojin ƙasa, da Sojojin sama da sauran hukumomin tsaro. An yi rugu-rugu da matattaran ‘yan ta’adda a Arewa Maso Gabas, wanda hakan ya yi sanadiyar raguwar hare-hare. A Arewa Maso Yamma kuwa, gagarumar gudummawa da ma’aikatar tsaro a ƙarƙashinsa ta amfani da ƙarfin soja ya yi mummunar illa ga matattarar ‘yan ta’adda wanda hakan ya kyautata fata da al’umma ke da shi cewa an kusan share musu hawaye.

  1. Kula da walwalar sojoji da ƙarfafa musu gwiwa

Ganin cewa ƙarfin Sojan Nijeriya ya dogara ne a rundunarta, Dakta Bello Matawalle ya inganta hanyoyin walwalar sojojin ta hanyar biyan su kuɗin alawus a kan lokaci, kyautata matsuguninsu, da kuma samun ingantaccen kiwon lafiya. Wannan ya ƙara azama wa sojojin da suke gwabza yaƙi a fagagen fama.

  1. Zamanantar da Dakarun Sojoji

Ganin buƙatar gaggawa da ke akwai na zamanantar da sojojin Nigeriya, Matawalle ya samar da waraka ta hanyar samar da sabbin makamai na zamani, da jirage marasa matuƙi don tattara bayanai da kuma kayan ayyuka da sojoji ke buƙata lokacin yaƙi.

Waɗannan kayayyaki sun inganta dabarun da sojoji ke amfani da su ta hanyar raguwar yawan sojojin da ke rasa rayukansu da kuma ƙaruwar nasarori a duk lokacin da aka fita ba-ta-kashi.

  1. Raguwar sace-sacen mai da zagon ƙasa wa tattalin arziki.

Tattalin arzikin Nijeriya ya jima na fama da illar da ake masa sakamakon satan ɗanyen mai a yankin Niger Delta. A ƙarkashin jagorancin Matawalle, an samu ƙaruwar aikace-aikacen da suka haɗa da haɗin gwiwar sojojin ruwa waɗanda suka haɗa da lalata cibiyoyin sace ɗanyen mai wanda hakan ya haifar da aruwar ɗanyen mai da ake fitar da kuma ƙarin kuɗaɗen shiga ga ƙasa.

  1. Karfafa mu’amala da haɗin gwiwa da ƙaware a yankin Afrika da ƙasa-da-ƙasa.

Yawancin matsalolin tsaro ya kan wuce iyakar ƙasa, saboda haka ne Dakta Matawalle bai yi ƙasa a gwiwa ba wurin ɗaukar matakan ƙulla ƙawance da makwabtan asashe irin su Chadi, da Nijar da Kamaru, da sauran ƙawayen ƙasashe irin su Amurka, Birtaniya da Tarayyar Turai wanda ya inganta yanda ake tattara bayanai da kuma musayar bayanan sirri. Hakan ya sa ‘yan ta’adda da masu aikata muggan laifuka ke samun wahalar samun maɓoya.

  1. Karfafa ƙere-ƙeren kayan yaƙi a gida

Bisa umurnin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar na tunanin dogaro da kai a fannin tsaro, Dakta Bello Matawalle ya yi ƙoƙarin agaza wa Hukumar Samar da Kayan Yaƙi ta Nijeriya (DICON) domin ƙara samar da makaman yaƙi a gida Nijeriya. Wannan mataki ya rage dogaro da ƙasashen waje da kuma ƙarfafa tattalin arzikin tsaron Nijeriya.

Baya ga ɓangaren yaƙi, Bello Matawalle yana cigaba da jaddada muhimmancin aiki da al’umma domin dawo da tsaro. Wannan kiranye da yake yi wurin neman tattaunawa, da sasanci da kuma ayyukan cigaba a yankunan da ake rikici sun taimaka matuƙa gaya wajen ɗinke rashin yarda tsakanin jami’an tsaro da kuma fararen hula, wanda hakan zai haifar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Jagorancin Bello Matawalle ya nuna aiki ba kama ƙafar yaro, sabbin dabaru, da kuma kishin ƙasa. Nasarorinsa ya nuna irin fahimtarsa a matsalolin tsaron Nijeriya da kuma irin niyyar da gwamnati ke da shi wurin magance su.

Bashir Aliyu ɗan jarida ne mai nazarin al’amuran da suka shafi siyasa da tsaro.

By ukarofi