Sa’o’i bayan naɗa ta, Tinubu ya maye gurbin Dakta Ɗankaka a FCC yayin garambawul ga ma’aikatansa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yayin wani juyin yanayi, Shugaba Bola Tinubu ya tsige Dakta Muheeba Ɗankaka daga muƙaminta na Shugabar Hukumar Tabbatar da Daidaito (FCC), sa’o’i kaɗan da naɗa ta, inda ya maye gurbinta da tsohuwar ƴar majalisa, Ayo Hulayat Omidiran.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya sanar da manema labarai hakan a wata takarda.

Omidiran, wadda ƴar majalisar wakilai ce har sau biyu daga jihar Osun, ta maye gurbin Dakta Ɗankaka, wadda aka nuna rashin amincewa da naɗin nata, kamar yadda kakakin ya bayyana.

Haka kuma, Tinubu a yayin garambawul ɗin ya naɗa Mohammed Musa a matsayin Sakataren hukumar, wanda ya maye gurbin Kayode Oladele, wato kwamishina daga jihar Ogun, kuma ya taɓa zama shugaban riƙo bayan dakatar da Ɗankaka a 2024.

Tinubu ya kuma sabunta naɗin Lawal Ya’u Roni (Jigawa), Abubakar Atiku Bunu (Kebbi), da Eludayo Eluyemi (Osun) a karo na biyu tare da Abdulwasiu Kayode Bawalla (Lagos).

Kazalika, Shugaban ƙasar ya naɗa sabbin kwamishinoni da za su wakilci jihohi har da Abuja, waɗanda suka haɗa da:

Hon. Obina Oriaku (Abia)

Mrs. Bema Olvadi Madayi (Adamawa)

Obongawan Dora Ebong (Akwa Ibom)

Hon. Nnoli Nkechi Gloria (Anambra)

Babangida Adamu Gwana (Bauchi)

Sir Tonye Okio (Bayelsa)

Aligba Eugene Tarkende (Benuwai)

Engr. Modu Mustapha (Borno)

Dr. Stella Odey Ekpo (Kuros-Riba)

Ederin Lovette Idisi (Delta)

Barr. Nwokpor Vincent Nduka (Ebonyi)

Hon. Chief Victor Sabor Edoror (Edo)

Hon. Sola Fokanle (Ekiti)

Peter Eze (Enugu)

Sauran sun haɗa da:

Ibrahim Baba Mairiga (Gombe)

Hon. Jerry Alagbaoso (Imo)

Ruth Jumai Ango (Kaduna)

Muhammad Awwal Nayaya (Kano)

Hon. Anas Isah (Katsina)

Bello Idris Eneye (Kogi)

Dr. Ibrahim Abdullahi (Kwara)

Alh. Isah Jibrin (Niger)

Comrade Ajimudu Bola (Ondo)

Prince Ayodeji Abas Aleshinloye (Oyo)

Hon. Pam Bolman (Filato)

Aaron Chukwuemeka (Ribas)

Alh. Aminu Tambar (Sakkwato)

Kwamared Bobboi Bala Kaigama (Taraba)

Hon. Jibir Maigari (Yobe)

Sani Garba (Zamfara)

Solomon Ayuba Dagami (Abuja)

Ana ganin naɗin Omidiran ya kawo sabon sauyi ga siyasa da gudanarwa a FCC duba da cewa ita ke da alhakin tabbatar da daidaito a harkokin naɗe-naɗen muƙamai a ƙasa.

By Babaji