
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu yana jagorantar zaman Majalisar Zartarwa FEC, a Faɗar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Ana gudanar da zaman ne a sashen majalisar.
Haka kuma, zaman ya ƙunshi Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, Sakataren Gwamnati Sanata George Akume, Shugabar Ma’aikatar Ma’aikata Didi Wilson-Jack, Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Femi Gbajabiamila da Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro (NSA) Nuhu Ribaɗu.
Gabannin zaman, Shugaba Tinubu ya naɗa Farfesa C.J Dakas da Dakta Uchenna Eugene a matsayin shugaba da kwamishina na Hukumar Gyare-gyaren Dokoki.
Sannan, a yayin fara zaman ne aka yi shuru na tsawo minti guda domin girmama marigayi Audu Ogbeh, wanda tsohon ministan noma kuma shugaban jam’iyyar PDP ne a Nijeriya. Ya rasu ne a makon da ya gabata bayan shafe shekaru 78 a duniya.
