Shugaban NULGE na Kano ya buƙaci ma’aikatan ƙananan hukumomi su ruɓanya ƙoƙari

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta Ƙasa (NULGE), reshen Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Muhammad, ya shawarci ma’aikatan ƙananan hukumomi a jihar su kasance masu zuwa aiki akan lokaci tare da jajircewa wajen sauke nauyin da ke kansu. Ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya kai ziyara sakatariyar Ƙaramar Hukumar Bichi a yau, inda ya yi tsokaci kan muhimmancin ƙauracewa sakaci da rashin tsayawa tsayin daka wajen inganta aikin gwamnati.

Kwamared Ibrahim ya ce manufar wannan ziyarar ita ce ƙarfafa gwiwar ma’aikata don su ƙara zage damtse. Ya jinjinawa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa sauraron koke-koken ma’aikatan ƙananan hukumomi, musamman wajen biyan albashi kan kari da kuma haƙƙokin ‘yan fansho. Ya bayyana cewa gwamnan ya ɗauki matakin ƙarin mafi karancin fansho zuwa N20,000, tare da biyan kuɗaɗen giratuti da suka kai sama da Naira biliyan 22 ga waɗanda suka yi ritaya.

A nasa jawabin, Shugaban ƙaramar hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ta bakin Daraktan Mulki da Kudi, Alhaji Abba Muhammad Diso, ya godewa shugabannin NULGE bisa wannan ziyara. Ya ce karramar hukumar tana aiki tuƙuru don tabbatar da biyan hakkokin dagatai da masu unguwanni, tare da tabbatar da cewa sunayen sabbin ma’aikata 125 sun riga sun tafi Ma’aikatar Kananan Hukumomi domin a saka su cikin tsarin biyan albashi.

Shi ma Sakataren Karamar Hukumar Bichi, Anas Muhammad Abdullahi, ya bayyana cewa an riga an warware matsalolin ma’aikatan karamar hukumar. Ya kuma yaba wa gwamnatin jihar da bankin bayar da lamuni bisa shirin samar da gidaje hamsin (50) ga ma’aikatan Bichi. Ya ce wannan aiki ya nuna jajircewar gwamnati wajen inganta walwalar ma’aikata a fannin gidaje da jin dadin rayuwa.

By ukarofi