Haɗin kan samar da tsaro na da tasiri ga al’umma – Hukumar Shari’a

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta gudanar da ziyarar aiki zuwa ofishin Babban Sufeton ‘Yan Sanda mai kula da shiyya ta ɗaya, AIG Garba Ahmed, domin ƙulla alaƙar aiki tare da ƙarfafa haɗin gwiwa a tsakanin ɓangarorin biyu.

Ziyarar wacce ta kasance ƙarƙashin jagorancin Shugaban hukumar, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, sun bayyana cewa na daga cikin matakan faɗaɗa dangantakar aiki da hukumomin tsaro, musamman wajen tabbatar da adalci, tsaro, da kiyaye dokokin ƙasa bisa ƙa’ida da tsarin addini da al’ada.

AIG Garba Ahmed ya yaba da wannan ziyara, inda ya nuna shirin rundunar ‘yan sanda na haɗin kai da Hukumar Shari’a wajen gudanar da ayyukan da suka shafi tsaro da kyautata zaman lafiya a Kano da sauran yankunan da shiyya ta ɗaya ke kula da su.

Sheikh Daneji yana tare da Kwamishina na ɗaya Gwani Hadi da Kwamishina na Biyu Sheikh Ali Danabba da mambobi da daraktoci na hukumar bakiɗaya.

By ukarofi