Majalisar Zartarwa ta ƙungiyar RTEAN ta dakatar da Sakatare Janar, ta kafa kwamitin bincike

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kungiyar Ma’aikatan Motocin Sufuri ta Nijeriya (RTEAN) na son sanar da mambobinta, masu ruwa da tsaki, da sauran jama’a cewa an gudanar da taron majalisar zartarwa na gaggawa (NEC) a ranar Laraba 13 ga watan Agusta 2025 a sakatariyar ƙungiyar, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙungiyar ya tanada da kuma ƙudirin yin gaskiya, da riƙon amana, a cikin shugabanci.

Taron ya kasance ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaba na ƙasa.

Muhammad Abu Bakr Bishara, yana bin izini bisa ga ƙa’idojin aiki na ƙungiyar.

A yayin taron, Majalisar ta NEC ta tattauna sosai kan al’amuran da suka shafi halin babban sakatare, Mista Yusuf Ibrahim Adeniyi. Bayan nazarin rahotannin da ake da su Majalisar ta yanke shawarar cewa ayyukan Mista Adeneyi sun haɗa da rashin ɗa’a da kuma cin amana.

Dangane da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin ƙungiyar, kuma domin kiyaye mutunci da haɗin kan ƙungiyar, Majalisar Zartarwa ta ƙasa bakiɗaya ta yanke shawarar dakatar da Mista Yusuf Ibrahim Adeniyi daga muƙamin babban sakatare ba tare da ɓata lokaci ba, har sai an kammala cikakken bincike.

Don haka ne dai Majalisar Zartarwar NEC ta kafa kwamitin bincike mai mutum bakwai da zai binciki duk wasu zarge-zarge da al’amuran da suka shafi lamarin. Kwamitin yana ƙarƙashin jagorancin Dr Barista Samuel Agbede yayin da Hon. Adamu Zubairu Jalaluddeen a matsayin sakatare kuma an umurce shi ya gabatar da sakamakon bincikensa da shawarwarinsa cikin watanni biyu.

Jagorancin RTEAN yana tabbatar wa dukkan membobi da sauran al’umma jajircewarsu na tabbatar da gaskiya da adalci wajen tafiyar da wannan lamari.

ƙungiyar ta ci gaba da mai da hankali kan manufarta na farko na inganta jin daɗin mambobinta da bunƙasa ci gaban harkar sufuri a Nijeriya.

Kwamitin binciken ya yi daidai da sashe na 6:2A(b-c) na kundin tsarin mulkin RTEAN kuma Mista Samuel Agbede ne zai jagoranta, yayin da Adamu Jalaluddeen a matsayin Sakatare.

Bishara ya ce sauran mambobin sun haɗa da Adamu Bulama, Alhaji Salman Ayoku, Cif Ifie Orabor, da Alhaji Musa Zuba.

“Sharuɗɗan kwamitin sun haɗa da bincikar duk zarge-zargen, gayyata da sauraron duk wani ɓangaren da abin ya shafa, da kuma gabatar da rubutaccen rahoton binciken da shawarwari ga majalisar zartarwa ta ƙasa cikin watanni biyu.”

Ya ce, har zuwa ƙarshen binciken, mataimakin babban sakataren ƙungiyar, Henry Ugwu zai yi aiki a matsayin muƙaddashin sakataren ƙungiyar.

Bishara ya ce kwamitin yana da hurumin neman takardu, gayyato shaidu, da kuma gudanar da dukkan ayyukan da suka dace domin sauke nauyin da aka ɗora masa.

By ukarofi