Daga ALI ABUBAKAR SADIK
\Allah ya ji kan wannan matashi Sadiƙ Gentle, hadimin kwankwasiyya. Wato ban san wannan matashi ba sai a Yan watannin nan sakamakon bayan na yi wani rubutu da ya dan yi shura sakamakon Jan hankali da na yi wa Madugun kwankwasiyya wasu ke ganin ba su ji dadin rubutun ba, musamman yan darikar, saboda taken rubutun ‘Kwankwaso a local champion zai kare’.
To, bayan nan ne sai na yi ta ganin hoton Sadiƙ Gentle ya na turo min domin na sahale ya zama abokina a Facebook. Na yi biris da bukatarsa na tsawon lokaci saboda na farko dai abokaina sun cika, idan zan saka wani sai na kori wani. Sannan ina shakkar ko ya na son yi min raddin rubutuna ne shi yasa.
Bayan wani lokaci dai da bukatar ke ta dawo min sai na bi shafinsa na duba irin abubuwa da ya ke sawa. Don haka sai na ga bari na amince masa. Tun da muka fara abotar Facebook bai taba min rashin kunya ba yadda wasu irinsa su ke. Kuma sai naga ya na bin wasu rubuce-rubuce na. Na ji tashin hankali shekaranjiya bayan samun labarin farmaki da aka kai masa.
Na yi ta bibiyar labarinsa har zuwa yau da safe da kwatsam na ji mutuwarsa. Allah ya sa wahalarsa kenan. Amin.
Gaskiya Gwamna da gwamnatin Kano na da bukatar canja taku yadda suke gudanar da mulkinsu musamman wajen kashe kudaden gwamnati. Hasarar wannan yaro a Kwankwasiyya ya kamata ya zama izina ga Gwamna cewa lallai wajibi ne idan har abinda suke iƙirari a baki ya Kai zuci a fara ganin yadda kudade da policies na gwamnati zasu karkata wajen talakawa. Matsalar rashin aikin yi ga matasa shine mafi girman kalubale da gwamnatin Kano ya kamata ta fuskanta. Rashin aikin yi na cikin dalilin da aka yi asarar Sadiƙ Gentle. Domin wadanda su ka far masa da su na da aikin yi wallahi zai wahala su zama ɓarayi.
Duk mai bibiya ya san cewa babu wata gwamnati tun daga 1999 zuwa yanzu da ta sami kuɗaɗe kamar wannan gwamnati. Fisabilillah ya za’a ce lokaci mafi talauci ga Kanawa amma ya zama maimakon lalubo hanyoyi da wadannan kudade zasu Isa ga talaka su rage talauci, su kawo tsaro, amma kullum sai ayi ta bijiro da manyan ayyuka na kyal-kyal banza da kalilan ne za su amfana ta harkar kwangiloli, kuma akasarin al’umma na cikin yunwa?
Kullum ina takaicin yadda na yi kokarin kawowa jihar Kano mutanen China da suke son su zo su zuba jari a dama-daman mu, amma abin ya ci tura bayan watanni na feasibility studies, sannan na gabatar wa kwamishinoni biyu bayani har da sakataren gwamnati, kuma na turawa Gwamna proposal ya sahale na zo na yi musu presentation a kyauta ban ce a biya ni ba. Amma duk aka yi biris da ni. Duk mai hankali ya san cewa Kano ba ta da kadarar da ta wuce ta Dams 22 da Allah ya bamu, kuma kowa shaida ne yadda Dam din Tiga kawai ya kawo arziki mara misaltuwa, ba ga kananan hukumomin Kura, Garun Malam, Rano, Bunkure, Tudun Wada da Doguwa ba kawai, hatta duk fadin Afirka ta yamma babu waje mai albarkar noma irin yankin, yadda ko almajirai na yankin baka gani a birnin Kano sakamakon tsawon shekara matasa na da abin yi. Dam daya fa kenan cikin 22. Mafi takaici kuma sai aka wayi gari cewa Gwamna ya sahale kusan biliyan 7 a gina sabon Dam a kunci, maimakon a saka kuɗin a raya wanda ake da shi.
A yau, matasa sun addabi birnin Kano da fadace fadace na daba kusan a kullum, sannan ana rasa rayuwar mutane irinsu Sadiƙ Gentle sakamakon kwacen waya da sata baya ga waɗanda ake nakasawa. A duk wata muna haihuwar mutane 27,000 a Kano, na yanzu mun kasa samar musu da abin yi, ina ga na gobe?
Kira ga Gwamna shine ya farka daga barcin da ya ke na cewa yayi kaso 85% na aikinsa, to wallahi ko kashi biyar bai yi ba, domin matasa basu da aikin yi, magidanta basa iya cin abinci kirki, Yara ba su da makarantu na gari. Gwamna ya daina biye tafin Yan abi yarima a sha kiɗa. Akwai sauran Jan aiki a gabansa kuma ba shi da tabbacin zai zarce a 2027. Ya kuma tuna da yadda Tarihi ya kasa mantawa da su Audu Bako da Rimi sakamakon ayyukansu na dindindin. Don Allah mutuwar wannan yaro naka na kusa da kai ya farkar da kai hadarin da al’ummar jihar Kano ke ciki, kuma ka gane bukatar saka kudadenmu wajen da muke bukata.
Yin haka shine kadai hanyar da zaka bar legacy abin tunawa kuma ya haifar mana da tsaro. A ƙarshe kuma ka tuna ko ka tambayi kanka, me yasa Kwankwasiyya ta zama darika kamar ta addini? Shin zanen jan fenti ne a kan rufin makarantu ko gadojin sama, ko kuma matasa da suka sami damammakin tafiya karatu a jami’in gida da waje ko mata da matasa da suka sami jari suka gina rayuwarsu? Da waɗanda suka shiga aikin gwamnati irinsu Karota?
ƙirƙirar hanyoyi samar da ayyuka zai habaka tattalin arziki, ya bunkasa kudaden shiga, samar da abinci kuma mafi mahimmanci ya kawo tsaro, yadda kowa idan zai ci ya ƙoshi kwakwalwarsa zata yi aiki ba zai shiga hanyoyin sharri ba na kwaya, yadda a yau Kano ta zartar kowa yawan masu ta’ammali da miyagun kwayoyi sakamakon dimbin matasa da ba su da aiki. Saura shekarar daya ya rage maka ka canza salon mulkinka yadda za mu so a ce ka zarce a 2027.
