Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jam’iyyar All Progressives Congress APC reshen jihar Zamfara ta bayyana zargin da jam’iyyar PDP ta yi na cewa APC ta ɗauki hayar jami’an soji a zaɓen ‘yan majalisar dokokin jihar ranar Asabar da ta gabata a Ƙaura Namoda ta Kudu tare da korar masu zaɓe daga rumfunan zaɓen su a matsayin ƙarya tsagwaron ta don ɓata sunan rundunar sojojin.
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na jihar Yusuf Idris ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ofishin sa a yau Litinin.
A cewarsa, jami’an tsaro an tura su a dukkan rumfunan zaɓe domin daƙile duk wani maguɗin zaɓe da lalata kayayyakin zaɓe domin kada su haifar da tashin hankali a lokacin zaɓe.
“Zarge-zargen da jam’iyyar PDP ke yi gaba ɗaya na zalunci ne kuma APC ta yaba da ƙoƙarin jami’an tsaro musamman ‘yan sanda, sibil defens da sojoji waɗanda suka yi aiki da kyau wajen ganin an dawo da zaman lafiya a zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata a Zamfara,” in ji Yusuf.
Ya zargi jam’iyyar PDP da yin amfani da jami’an tsaron al’umma mallakin gwamnatin jihar CPG, ‘yan banga da Kuma ‘yan bangar siyasa ta hanyar haddasa tashin hankali a lokacin zaɓen ƙarƙashin jagorancin shugabannin ƙananan hukumomin Gusau da Talata Mafara.
“Muna da komai a rubuce lokacin da shugabannin ƙananan hukumomin biyu suka jagoranci ƙungiyoyin da na ambata a baya a garuruwan Bela, Kurya Madaro da Sakajiki suka lalata kayayyakin zaɓe mallakar hukumar zaɓen ta Ƙasa INEC.” Yace
“Zargin da jam’iyyar PDP ta yi na ƙoƙarin ɗaukar nauyin sojoji a lokacin zaɓen ba gaskiya bane, Domin sojojin Najeriya na sadaukar da rayuwarsu a kullum don kare al’umma daga hare haren ‘yan bindiga a jihar”.
“Muna kira ga jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara ta kawo shaidar ta na zargin jam’iyyar APC na da hannu wajen tada hargitsi lokacin zaɓen cike gurbin ɗan majalisar dokokin jihar a ranar Asabar da ta gabata”. A cewar Yusuf Idris
Jam’iyyar ta yi kira ga jami’an tsaro a jihar da su ɗore da ɗan lokaci wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa.
A cewarsa, APC za ta ci gaba da kasancewa mai bin doka da oda da kuma kare martabar dimokuraɗiyya a kowane lokaci a jihar.
Yusuf ya ƙara da cewa, APC za ta yi nasara a zaɓen da za a sake gudanarwa na cike gurbi a jihar ba tare da wata fargabar jam’iyyar PDP mai mulki a jihar ba.
