Ma’aikatar lafiya ta Zamfara da bankin duniya sun horar da jami’an kiwon lafiya

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau

Ma’aikatar lafiya ta Jihar Zamfara, tare da haɗin gwiwar hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jiha a ƙarƙashin tallafin bankin duniya (IMPACT Project), sun gudanar da horon kwanaki biyu ga jami’an kiwon lafiya don tsarin kula da harkokin kiwon lafiya kan yadda za su gudanar da adana bayanan tsarin bayanan kiwon lafiya a matakin gundumomi (DHIS2) a zamanance.

Haka zalika an samar da na’ura mai aiki da ƙwaƙwalwa (Laptop kwamfutar tafi-da-gidanka) ga kowane daga cikin cibiyoyin kiwon lafiya 174 don tattara bayanai a zamanance.

Horon wanda aka gudanar a otel ɗin Karma dake Gusau, an tsara shi ne domin ƙarfafa tsarin kula da harkokin kiwon lafiya na ƙasa (NHMIS) ta hanyar na’ura mai aiki da ƙwaƙwalwa don samun ingantattun bayanan kiwon lafiya daga cibiyoyin kiwon lafiya 147 ƙarƙashin shirin IMPACT Project da Basic Healthcare Provision Fund (BHCPF) a faɗin jihar.

Da yake jawabi a wajen rufe taron a ranar Lahadin da ta gabata, shugaban hukumar kula da lafiya matakin farko na jihar Dakta Hussaini Yakubu Anka, yace shirin na da nufin bai wa mahalarta taron sanin makamar aiki da tattaro bayanai a zamanance, shigar da bayanai a yanar gizo da bayar da rahoto, da kuma tantance bayanai don tabbatar da ingantaccen tsari kiwon lafiya a jihar.

Shugaban shirin IMPACT Project a jihar, Dakta Iliya Sale Ahmad, ya gargaɗi mahalarta taron da su guji yin amfani da kwamfutocin da aka tanadar ba bisa ƙa’ida ba, inda ya bayyana cewa, na’urorin hukumar ZITDA ce ta samar dasu domin cigaban kiwon lafiya a Jihar Zamfara .

Haka zalika yayi gargaɗin cewa duk wata asara ko ɓarna ga na’urorin za a ɗora alhakin faruwar hakan ga jami’in kiwon lafiyar da abin ya shafa, inda ya buƙaci mahalarta taron da su yi amfani da kwamfutocin don adana bayanan tsarin kiwon lafiya sahihi.

Shima a nasa jawabin, wakilin hukumar kula da lafiya a matakin farko ta ƙasa (NPHCDA), Salisu Attahiru Jega, ya bayyana horon a matsayin wani ɓangare na ministan lafiya don tabbatar da samar da rahotanni kan DHIS2.

Ya yi nuni da cewa, shirin zai rage jinkiri wajen bayar da bayanai, tare da adana su a hukumance a dukkanin cibiyoyin kiwon lafiya 174 dake jihar.

Jega ya kuma ja hankalin mahalarta taron da suyi amfani da horon da su ka samu a cibiyoyin kiwon lafiya da suke wakilta.

Ya kuma jaddada buƙatar kiyaye kwamfutocin da kuma la’akari da muhimmancin su.

By ukarofi