Daga ADAMU YUSUF INDABO a Kano
Fitacciyar marubuciyar Hausa daga Jahar Bauchi da ke Arewacin Najeriya, wato Sadiya Nasir Dan, ta yi wannan furuci ne tare da jan kunnen marubuta musamman marubutan yanar gizo da su tsaftace alƙalumansu ga barin rubuta abubuwa marasa amfani, da dukkan abun da bai dace ba a tarbiyyar Musulunci da al’adar Malam Bahaushe. Marubuciya Sadiya Nasir Dan, ta yi wannan kira ne a yayin da suke tattaunawa da wakilinmu Adamu Yusuf Indabo. Ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance:
MANHAJA: Da farko dai mene ne cikakken sunan marubuciyar, da kuma taƙaitaccen tarihin rayuwarki?
SADIYA: Sunana Sadiya Nasir Dan haifaffiyar garin Bauchi, an haife ni a ranar 24/8/ shekara ta 1995. Matakin karatu na yi Diploma a masscom. Na yi primary school ɗina a Fomwan, sannan na yi secondary school ɗina a Sky Crest, na yi Diploma ta a Abubakar Tatari Ali polytechnic da ke cikin garin Bauchi.
Masu karatu za su so jin tarihi da kuma gwagwarmayarki a duniyar rubutu?
To kamar dai yanda na faɗa ni haifaffiyar Garin Bauchi ce, na jima ina sha’awar rubutu, tun ina secondary school nake rubutawa a littafi, na zo na watsar saboda yanayin rayuwa girma na shiga. To abin ya dawo min ne a shekara 2020 bayan kammala diploma ta a ɓangaren aikin jarida, na ƙara samun eɗperience sosai da ya dawo min da sha’awar rubutu, wannan dalilin ya sa na mai da hankali. Gwagwarmaya ana nan ana yi har gobe, zaka samu masoya kuma za ka samu maƙiya, amma Alhamdulillah ni dai har a yanzu da nake magana ba zan ce na ga maƙiyina a fannin rubutu ba, saboda Allah ya haɗa ni da mutanen arziki wanda ba su da hassada masu kirkin gaske.
To ɓangaren karatun addini fa, kuma ya batun iyali?
Karatun Addini na yi daidai gwargwado ta fannin sanin littafai, sannan na hadda ce ƙur’ani Mai tsarki tun ina shekara ‘yar shekara sha biyar (15). Na yi aure a shekara 2018, Allah ya azurta ni da yarinya sunanta Aisha.
ko za ki iya tuna wanne littafi ne na farko da kika fara rubutawa a wancen lokacin, kuma wanne darasi littafin yake koyarwa?
‘Karfa’ shi ne littafina na farko da na fara rubutawa a cikin shekarar 2020, kuma Alhamdulillah na yi ƙoƙari a matsayinsa na littafin farko da har na iya kammala sa ba tare da jagora ba. Littafin ya ƙunshi darasu da dama, saboda labari ne a kan illar ƙiyayya, da kuma yanda Allah ke canza al’amarin sa wanda ake ganin ba komai ba ne ya zamo komai. Sai kuma illar bin bokaye da malaman tsubbu yanda abin yake zuwa daga ƙarshe babu kyan gani.
To cikin shekaru biyar da fara yin rubutunki, zuwa yau littafai nawa kika rubuta?
Na rubuta littafai ne guda goma, su ne: ‘Karfa’, ‘Sanadin Son Zuciya’, ‘Mugun Gani’, ‘Kuɗin Jini’, ‘Jan Kunne’, ‘Iyalaina’, ‘Kuluwa’, ‘Bishiyar Tsiya’, ‘Hatsabibiya Meenah’, ‘Rikon Sakaina’. Waɗannan littafai guda goma su ne na rubuta su cikin shekaru biyar baya zuwa yau. Amma waɗanda na rubuta lokacin ina makaranta tuni na watsa su a kwandon shara saboda ba komai a cikin su face mafarkai da burika da shirme irin na ƙuruciya. Shi ya sa bana sanya su cikin lissafi.
To a cikin waɗannan littafai naki guda 10 wanne ne bakandamiyarki, kuma me ya ƙunsa?
Sanadin Son Zuciya’ shi ne bakandamiyata. Labari ne da na sha baƙar wahala wajen rubutawa, labari ne da ya ƙunshi aljannu da kuma daji, ta yanda ɗan adam ke tsintar kansa hanun aljannu da gwagwarmayar da ke fuskanta. Darasin da yake koyarwa shi ne: Illar son abin duniya da rashin mutunci ko in ce rashin kunya.
To ya batun ƙungiyar marubuta?
E ina cikin ƙungiyar marubuta ta Haske Writers Association a ƙarƙashin jagorancin shugabar ƙungiyar marubuciya.
Marubuta da yawa asalinsu makaranta ne, shin ke ma kin yi karance-karancen littafan Hausa ne ko ya?
E na yi sosai ma, ko in ce ina ma kan yi, don har yanzu idan littafi ya mini ina karantawa har ƙarshe har ma ina saya da kuɗina.
To cikin marubutan wacce ce gwanarki da ba kya fashin karanta littafanta?
Babbar gwanata a cikin marubuta ita ce Ayusher Muhammad.
Kuma ya za ki kimanta marubutan da, da kuma marubutan wannan zamanin ta fuskar ƙwarewa da kuma ilimantarwa?
Eh to gaskiya duka ɓangare biyun nan sun taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasar adabi da al’adun Hausa. Amma gaskiya marubutan baya sun fi. Domin nagartar tunanin magabatanmu da na wannan lokacin akwai tazara a tsakaninsu tazara mai nisan gaske. Domin kuwa sun fi zuwa da karkata akalar rubutunsu kan asalin hausawan da ɗabi’u da kayyaki na gargajiya, saɓanin na yanzu da suke zamanantar da komai da kuma koyawa mutane rayuwa mai tsada, yayin da wani littafin ma rabinsa Turanci rabi Hausa.
Cikin wanne yanayi da kuma lokaci marubuciya Sadiya ta fi jin daɗin yin rubutu?
Na fi jin daɗin yin rubutu da safe, kamar daga ƙarfe shida zuwa ƙarfe 10. Yanayi kuma in dai zan samu waje shiru babu hayaniya, to nan da nan basira ke zuwa mini kamar wahayi.
A cikin marubuta, wacce ce ta hannun damarki, da koyaushe za a iya samun labarinki a wajen ta?
Aminiyata mafi kusaci da ni ita ce marubuciya Zainab Bawa, wato Zainab Muhammad Bawa, marubuciyar littafin ‘Bibiya Ta Ake Yi’.
To daga fara rubutunki zuwa yau, waɗanne nasarori kika cimma ta fuskar rubutu?
Nasarori ba za su ƙirguwa ba gaskiya, sai godiya ga Allah kawai. Duk lokacin da zan fitar da littafi kafin na fitar zan yi ta tunani kamar ba zai yi farin jini ba, to Alhamdulillah da na fara kuma sai na samu mabiya da yawa. Don haka nasara kullum gaba take yi.
To ƙalubale kuma fa?
ƙalubale a littafin kuɗi na fi samu, ka san yanayin mutane, to akwai masu uzuri akwai wanda ba su da shi, akwai wanda idan laluri ya same ka don ya saya littafi shi ke nan ya samu damar da zai faɗa maka magana yanda ransa ya so. Ba ruwansa da cewa kasuwanci halas ne ba haramun ba.
Kin san rubutu fanni-fanni ne. Ke a wanne fanni kika fi ƙwarewa?
Labarin soyayya. Da kuma labarin gwagwarmayar fama da rayuwa da ke faruwa a zahirance.
Wanne kira kike da shi ga ‘yan uwanki marubuta?
Su ji tsoron Allah wajen isar da saƙo, su sani akwai ranar da Ubangiji zai tashe mu ya tambaye mu a kan abinda muka rubuta, don haka yana da kyau muna kiyaye alƙalumar mu wajen furta abinda ya dace. Mu guji rubutun batsa, domin gaskiyar lamari babu uzuri a rubutun batsa.
Wanne saƙo kuma kike da shi ga masoyanki masu bibiyar rubutunki koyaushe?
Ina ƙaunar su, ina alfahri da su domin duk matsayin da na taka su ne suka taka muhimmiyar rawa, Allah ya ƙara mana ƙaunar juna da fahimta.
To a rayuwa wanne abu kika fi so, kuma wanne abu kika fi tsana?
Ina matuƙar son mutum mai gaskiya da riƙon amana. Kuma na tsani munafurci matuƙar tsana, haka ma ƙarya da fuska biyu.
Kuma wanne irin abinci kika fi so?
Tuwo da miyar taushe.
To Hajiya Sadiya muna godiya.
Ni ce da godiya babban ɗan jarida. Kuma ina maka fatan alheri. Allah Ya ɗaukaka ku Ya ɗaukaka wannan gidan jarida na Blueprint Manhaja, amin
