Ambaliya: Yadda jihohin Arewa suka shiga uku

Spread the love

*Ta halakar da mutum 165

*Ta shafi mutane 119,0000

*Ta lalata gonaki 8,200

*Mutum 43,936 sun rasa matsuguni

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD a Kaduna da JAMIL GULMA a Birnin Kebbi 

Nijeriya, musamman a arewacin ƙasar, na fama da ɗaya daga cikin manyan bala’o’i a duniya ta ambaliyar a cikin ‘yan shekarun nan, inda aka tabbatar da mutuwar mutane aƙalla 165, yayin da ta shafi wasu sama da 119,000 cikin jihohi 19 na ƙasar ya zuwa ranar 16 ga Agusta, 2025.

Rrahoton Hukumar Gidan Talabijin ta Nijeriya (NTA) ce ta bayyana wannan ƙididdigar ta hanyar asusunta na ɗ, wanda ta ba da cikakken bayani kan ambaliyar ruwa ta 2025.

A cewar sanarwar, mutane 82 sun ɓace, 138 suka jikkata, sannan 43,936 suka rasa matsugunansu.

Ambaliyar ta ratsa cikin al’ummomi, gidaje, filayen noma, da muhimman ababen more rayuwa. Kimanin gidaje 8,594 ne suka lalace ko kuma nutse a ruwa, yayin da gonaki 8,278 suka lalace, lamarin da ya ƙara taɓarɓara yanayin ƙarancin abinci a Nijeriya.

Alƙaluman ƙididdigar sun ba da labarin waɗanda abin ya shafa, inda ya shafi: yara 53,314, mata 36,573, maza 24,600, tsofaffi 5,304, da nakasassu 1,863, wanda nuna irin yadda ya shafi al’ummomi masu rauni.

Jihohin da lamarin ya fi ƙamari sun haɗa da Imo, Ribas, Abia, Borno, da Kaduna, inda rahotanni suka ce an yi asarar rayuka da dama.

Sauran jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Borno, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Kogi, Kwara, Niger, Ondo, Ribas, Sakkwato, da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.

A taƙaice dai ƙananan hukumomi 43 ne suka samu rahoton ambaliyar ruwa, lamarin da ya sa ƙananan hukumomin suka cika da yawa.

Wakilin Blueprint Manhaja ya ruwaito cewa, dubban magidanta da iyalansu ne suka rasa matsugunansu tare da asarar amfanin gona na milliyoyin kuɗi sanadiyyar ambaliya a waɗansu sassan Jihar Kebbi.

Yanzu haka dai Gwamnatin Jihar Kebbi a ƙarƙashin jagorancin Malam Nasir Idris ta naɗa wani kwamiti ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ayyuka, Hon. Abdullahi Umar Faruk Muslim, don zagayen gani da ido tare da tantance adadin da ɓarnar da ruwan ya yi, don ɗaukar matakin gyara, saboda mutane su ci gaba da lamurransu na yau da kullum.

Da ya ke yi wa manema labarai bayani, Kwamishinan Yaɗa Labarai, Hon. Yakubu Ahmed Birnin Kebbi, ya bayyana cewa, akwai buƙatar Gwamnatin Tarayya ta gaggauta kawo agaji a jihar ta Kebbi, musamman a ɓangaren gyaran babbar gadar da ke kan babbar hanyar da ta haɗa jihohin Sokoto, Kebbi da Neja zuwa Legas da ke garin Liba, inda lamarin ya yi sanadiyyar zagaye mai nisa, domin yankewar gadar. Haka zalika, akwai gadar da haɗa garin Birnin Kebbi da Maƙera zuwa Kangiwa har zuwa Jamhuriyar Nijar da kuma hanyar da ta haɗa garuruwan Fana zuwa ɗakingari a ƙananan hukumomin Dandi da Suru.

Ya ƙara da cewa, yanzu haka akwai waɗansu manyan motocin ɗaukar kaya gida uku da ruwan ya tafi da su sanadiyyar faɗawa a cikin ɗaya daga cikin gadojin, wanda ya yi sanadiyyar asarar dukiyoyi masu yawa.

A Jihar Sokoto da ke maƙotaka da Kebbi kuwa, rahotanni daga ƙananan hukumomin Shagari da Boɗinga suna nuni da an sami iftila’in ambaliya da ya yi sanadiyyar asarar amfanin gona da rushewar gidaje da dama a yankunan Darhela da Bukutu a mazaɓar Toma da ke ƙaramar Hukumar Boɗinga. Sai kuma Dandin Mahe da ke ƙaramar Hukumar Shagari.

Rahotanni sun nuna aƙalla sama da gonaki 300 suka halaka a garin Badau, inda waɗansu 75 kuma a Butuku.

Jami’an hukumar ba da agaji ƙarƙashin jagorancin Malam Mustapha Umar sun kai ziyarar gani da ido, inda Sarkin Yamman Badau, Alhaji Alhaji Ibrahim Buda, ya bayyana musu cewa, gaskiya wannan lamarin ba ƙaramin bala’i ba ne, duk da ya ke Allah ya sa abin ya zo da sauƙi sanadiyyar aikin hanyar da Gwamnatin Jihar Sokoto ke yi, ya sa ɓarnar ruwan ta zo cikin sauƙi.

Haka zalika ruwan ya rushe gidaje da dama a unguwar Shiyyar Taba da kuma sama da gonaki 75.

Girman bala’in ya haifar da kira na gaggawa daga ƙungiyoyin agaji da gwamnatocin jihohi, don samar da abinci, matsuguni na wucingadi, tallafin  jinya da na jinƙai ga iyalan da suka rasa matsugunansu.

Shugabannin al’umma sun ce, a halin yanzu da dama daga cikin waɗanda abin ya shafa na samun mafaka a makarantu, coci-coci da sansanonin wucingadi, inda cunkoson jama’a ke ƙara haifar da fargabar ɓarkewar cututtuka na ruwa.

ƙwararru kan kula da bala’o’i sun yi gargaɗin cewa, lamarin na iya ƙara ta’azzara yayin da ake ci gaba da daminar bana. Al’ummomin da ke gefen koguna, gaɓar ruwa da kuma wuraren da ke kwance suna cikin shirin ko-ta-kwana.

Hukumomin gaggawa na Gwamnatin Tarayya ba su fitar da wani ingantaccen tsarin ɗaukar mataki na ƙasa ba, amma masu lura da al’amura na ganin lokaci ya ƙure.

Ambaliyar ruwan da ke zuwa a cikin ƙalubalen tattalin arzikin da ’yan Nijeriya ke fuskanta, ta janyo ana ƙara kira kan inganta manufofin daidaita yanayi da muhalli da kuma ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatoci da masu ruwa da tsaki kan harkokin jinƙai.

By ukarofi