Isra’ila ta bayyana cewa ta shiga sabon mataki na yaƙin da ta kira “Operation Gideon’s Chariots” a Gaza City, wanda ya ƙunshi faɗaɗa farmakin soja a birnin da ya kasance cibiya ta Hamas. Mai magana da yawun rundunar sojin Isra’ila, Effie Defrin, ya ce za su ƙara matsa lamba kan Hamas da kuma shirin kammala murƙushe ƙungiyar.
Shugaban Benjamin Netanyahu, ya bayar da umarni cewa a gaggauta wannan farmaki don a mamaye birnin da ya ƙunshi ɗaruruwan dubban fararen hula da ‘yan gudun hijira. Hamas ta bayyana wannan mataki a matsayin “raini ga ƙoƙarin sulhu da yarjejeniyar tsagaita wuta” da ake tattaunawa.
Isra’ila ta kira ƙarin sojojin 60,000, yayin da dubban Falasɗinawa suka fara tserewa daga Gaza saboda tsoron sabbin hare-hare. Ministan harkokin wajen Jordan, Ayman Safadi, ya soki Isra’ila da cewa tana haifar da “kisan gilla da yunwa”, lamarin da Faransa da Jamus su ma suka gargaɗin zai iya kawo barazana ga zaman lafiya. Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya kira shi “babban bala’i” da zai iya jefa yankin cikin yaƙin da ba ya ƙarewa.
A lokaci guda kuma, Isra’ila ta amince da sabon gina matsugunin haramtacce a West Bank (E1), wanda zai raba yankin biyu. Ministan harkokin wajen Birtaniya, David Lammy, ya bayyana wannan a matsayin tauye dokar ƙasa da ƙasa da kuma rushe mafarkin kafa ƙasa biyu. Majalisar ɗinkin Duniya da sauran ƙasashe sun nuna damuwa, yayin da Isra’ila ke ƙara samun suka daga ƙasashen duniya.
