
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Oba Akeem Owoade, wanda shi ne Alafin na Oyo ya bayyana cewa, shi ba mutum ne mai gasar iko ba da kowane sarki a ƙasar Yarbawa ko kuma a wani waje na daban.
Sarkin ya faɗi haka ne a wata takarda da Daraktan yaɗa labaransa, Bode Durojaiye ya fitar kan rashin jituwa da ke tsakanin sa da Ooni na Masarautar Ife, wato Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi.
Rikicin nasu ya samo asali ne a lokacin da Oonin ya bada sarautar Okanlomo ga wani ɗan kasuwa mai suna Dotun Sanusi yayin ƙaddamar da shafin gargajiya a Soshiyal Mediya da aka yi laƙabi da 2geda a wani otal mai suna Ilaji Hotel a Ibadan.
Durojaiye ya bayyana cewa, Alafin sarki ne mai jajircewa akan al’adunsu na yarbawa da ke fifita walwalar al’ummarsa, tsaro da ci-gabansu.
Ya kuma ce, ba zai taɓa sayer da al’adarsa ko ci-gaban al’ummarsa ba da wani kuɗi ɗan kaɗan, yana mai cewa kare martabar al’ummarsa shi ya fi masa akan komai.
