APC ta lashe zaɓen Ƙaura Namoda ta Kudu

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar APC ta lashe zaɓen majalisar dokokin jihar a Ƙaura Namoda ta Kudu inda Jamilu Sa’idu Kasuwar Daji ya zama wanda ya lashe zaɓen.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen, jami’in zaɓen, Farfesa Lawal Sa’ad na jami’ar tarayya Gusau, ya bayyana cewa Kamilu Sa’idu ya samu ƙuri’u 8,182 inda ya doke Muhammad Lawal na jam’iyyar PDP wanda ya samu ƙuri’u 5,543.

Hukumar INEC ta bayyana Kamilu Sa’idu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

“Kamilu Sa’idu na jam’iyyar APC, da ya samu mafi yawan ƙuri’u, an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasarar zama zaɓaɓɓen ɗan majalisar Jihar Zamfara,” in ji Farfesa Sa’adu.

Hakazalika, Sanarwar ta biyo bayan sake gudanar da zaɓukan ne a runfuna guda biyu a dake garin Sakajiki da kuma runfuna uku a ƙauyen Kyambarawa.

Da yake zantawa da manema labarai, mataimakin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, AIG Hassan Mohammed Gumel ya bayyana zaɓen da aka gudanar a matsayin cikin lumana.

AIG Gumel ya yabawa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro kan yadda suka tabbatar da bin doka da oda a lokacin zaɓen ta hanyar tabbatar da gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.

Shima da yake jawabi, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Maru da Bungudu Hon. Abdulmalik Zubairu ya bayyana zaɓen a matsayin sahihin zaɓe.

Hon. Zubairu ya bayyana nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaɓen a matsayin abin gagarumar nasara tare da bayyana cewa mulki zai dawo ga jam’iyyar APC a shekarar 2027 da ikon Allah.

By ukarofi