Hukumomi sun tsare wata ‘yar Kano bayan da ake zargin jirgin Ethiopia da canja mata jaka mai wiwi a ciki

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hukumomi a ƙasar Saudiyya na tsare da wata mata ‘yar jihar Kano, Maryam Hussaini Abdullahi, bayan da ake zargin kamfanin jirgin sama na Ethiopia, wato Ethiopian Airline ya musanya jakar ta da wata mai ɗauke da tabar wiwi.

Manhaja ta rawaito cewa Maryam ta tafi Saudiyya tare da mijinta, Abdullahi Baffa, don yin Umrah a ranar 6 ga Agusta, amma daga bisani aka tsare ta a Makkah bayan ‘yan sanda sun danganta ta da wata jakar “Ghana-must-go” cike da kayan da ake zargi na ƙwaya ne.

Mijinta, Abdullahi Baffa, ya ce sun tafi Saudiyya da matar sa kowa da jaka ɗaya, amma bayan isowarsu Jiddah, sai ba su ga nasu kayan ba. 

A cewar Baffa, ya shigar da ƙorafin ɓatan jakunkunan nasu inda aka basu don su ka cike aka kuma ce su jira sai hakan awanni 24.

Sai ya ƙara da cewa sai da ya yi haniya daga bisani aka ce masa ai haka jaridar ta ke, inda daga nan su ka wuce Madinah su ka sayi wasu kayan na amfaninsu a can.

“Bayan kwanaki 8, sai aka kira ni aka ce wai an ga ɗaya daga cikin jakunkunan namu saboda haka mu je mu karɓa. Sai na ce musu kawai a aika Nijeriya ma karɓa a can.” 

Baffa ya ce sun zo dawowa ne tun a filin jirgin sama na Jeddah, bayan an kammala tantance shi sai ma’aikatan Ethiopian Airline suka faɗa masa cewa an riƙe matarsa, sannan suka ce ya je cibiyar kula da masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ta Saudi Arabiya domin ƙarin bayani.

Ya ce daga nan ne ya tuntuɓi ofishin Jakadancin Nijeriya a Saudiyya inda ya samu taimakon da ya dace.

Ya zargi kamfanin jirgin da haɗa musu da wannan jaka ba tare da saninsu ba.

Baffa ya ce bayan sun shigar da ƙorafi a Jiddah, sai daga baya aka sanar da shi cewa ɗaya daga cikin jakunkunan ta iso, amma ya ƙi karɓa, ya nemi a mayar da shi Nijeriya. 

Baffa ya ce matarsa ta tabbatar masa cewa an nuna mata jaka cike da kayan da ba ta san komai ba a kansu.

Ya yi zargin cewa kamfanin jirgin yana ƙoƙarin ɓoye gaskiya kan lamarin. Ya kuma nemi gwamnatin Nijeriya ta gaggauta shiga tsakani domin kuɓutar da matarsa.

Kamfanin jirgin na Ethiopian Airlines ya tabbatar da cewa an fara bincike kan lamarin, yayin da ofishin jakadancin Nijeriya a Jiddah ya ce sun karɓi rahoton kuma bincike yana gudana.

Lamarin ya tunatar da na Zainab Aliyu a 2018, wacce aka tsare a Saudiyya bisa irin wannan zargi, kafin daga baya aka gano cewa ba ta da laifi.

By ukarofi