Gwamna Sule ya raba motoci masu aiki da wutar lantarki ga mabuƙata a Nasarawa

Spread the love

DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya

Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya raba wasu sabbin motocin zamani masu aiki da wutar lantarki guda 50 da wasu adaidaita sahu suma masu aiki da wutar lantarki 100 ga matasa da marasa galihu don bunƙasa tattalin arziki da kuma samar da ayukan yi a jihar.

Gwamna Sule a jawabin sa yayin da yake rarraba motocin ga waɗanda suka amfanar a Lafia, fadar jihar ya bayyana cewa rabon na da manufar samar ma waɗanda suka amfana ɗin damar gudanar da ayukan sufuri da motoci da kuma adaidaita sahun a matsayin kasuwanci, don haka zai rage matsalar rashin aikin yi.

Ya bayyana cewa motocin da adaidaita sahun da gwamnatin sa ta sayo duk na zamani ne dake amfani da wutar lantarki maimakon man fetur ko iskar gas.

Sule ya ƙara da cewa tuni gwamnatin jihar ta riga ta kafa cibiyar caji a wasu sabbin wurare a Lafiya da wasu sassan jihar don a rika caja motocin da adaidaita sahun lokaci-lokaci.

“Za mu kuma gina cibiyar caji ɗaya a kowanne daga cikin ƙaramar hukumar Akwanga da Keffi domin hidimar mazaɓu na Arewa da Yamma na Jihar Nasarawa,” Inji gwamnan.

Sule ya ƙara da cewa har ila yau za a gina wasu cibiyoyin caji a sauran ƙananan hukumomin jihar nan gaba.

A cewarsa za a fara turo motocin da adaidaita sahun birnin Lafiya ne da Akwanga da Keffi domin kai ma’aikatan gwamnati zuwa ofisoshinsu ne domin rage matsalar tattalin arziki da ake fama da ita a yanzu.

Hakanan za su yi hidima ga cibiyoyin ilimi a wurare uku, ciki har da jami’ar tarayya ta Lafia, kwalejin ilimi, Akwanga, da jami’ar jihar a Keffi don kwasan ɗalibai da malamai zuwa makarantun da sauran su.

Gwamnan a ƙarshe sai ya jaddada cewa dukkan motocin da adaidaita sahun suna amfani da wutar lantarki, sun kuma dace da gudanar da ayyuka na tsawon ranakun kwana ɗaya bayan an caje su inda ya bayyana begen sa cewa wannan shiri ba kawai zai samar da matsuguni ga waɗanda suka amfana kaɗai ba, har inganta rayuwan su baki ɗaya zai yi.

By ukarofi