
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hon. Alfred Emberga ya zama sabon kakakin majalisa a Majalisar Dokoki ta Jihar Benuwai.
A yau Lahadi aka rantsar da shi jim-kaɗan bayan da tsohon kakakin, Hyacinth Dajoh ya yi murabus.
A safiyar ranar Dajoh ya sanar da yin murabus daga muƙamin a wata takarda, lamarin da ya kai Emberga, wanda ke wakiltar mazaɓar Makurɗi ta Arewa kan muƙamin.
Dajoh ya yanke shawarar sauka daga kujerar ne bayan dakatar da mambobin majalisar huɗu da aka zarge su da yunƙurin tsige shi.
Waɗanda aka dakatar sun haɗa da Alfred Berger, Terna Shimawua, Cyril Ekong da James Umoru.
Da yake tsokaci akan batun, Gwamna Hyacinth Alia na jihar ya nesanta kansa daga rikicin, inda ya ce ba shi da hannu a zargin shirin cire Dajoh a matsayin kakaki.
Hakan na ƙunshe a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Sakataren yaɗa labaransa, Tersoo Kula inda ya tabbatar da cewa gwamnan ba shi da hannu a cikin al’amarin.
