Ɗabi’a ce irin tamu

Spread the love

Daga SUFYAN LAWAL KABO 

Yana daga cikin ɗabi’a na ƴan Arewa, bama ɗaukar mataki na kawar da musibar da ta tinkaro mu sai abu yazo ya ta’zzara yafi ƙarfinmu. Sai abin ya kai ga zub da jini, an shiga bala’i sannan ne za’ayi ta ihun cewa a matsa da addu’a. 

-Haka akayi sadda Boko Haram ta bullo, aka mayar da abin wasa. Manyan Arewa ciki har da Malaman Addini kowa yaja baki yayi shuru, wasu sabida tsoro wasu saboda siyasa, wasu sabida basu abin ke shafa ba.

-A zamanin Buhari ta’adanci da satar mutane ya tsananta, aka ƙi daukar mataki tun wuri har abin yazo ya zame mana bala’i. A yanzu an ta’adda na ƙone garuruwa, su ƙone mutane kurmus ciki har da mata da yara, su ƙone kayan abinci, suyiwa mata fyaɗe a gaban mazaje da ƴaƴan su, su farke cikin mata masu ciki, su sace mutane su kai daji domin su karbi fansa…. waiyazubillahi! 

-Ana cikin wannan, faɗan daba, da ƙwacen waya ya ta’azzara. Da farko, barazana suke yiwa mutune da muggan makamai su ƙwaci waya, da suka ga babu wani mataki da ake ɗauka a kansu, hasalima iyayensu ne da gurbatattun ƴan siyasa ke karbo su idan an kama su, sai suka dawo kashe mutane su kwaci wayoyi. Tun farko da an dauki tsatsauran mataki a kansu, an ayyanasu a matsayin ƴan fashi ana yanke musu hukuncin kisa, da ala’marin bai ta’azara ba yadda yake a yanzu. 

Muna cikin wannan, sai ga wata sabuwar musibar ta bullo. Tinubu ya gayyato Isra’ila, haramtacciyar ƙasar da hatta wasu ƙasashen da ba na Musulmi ba, sun aiyana ta a matsayin ƴar ta’addar ƙasa dake aikata munanan ta’adanci ga Musulmi a duniya, amma sabida siyasa, munafurci da kwaɗayi, malaman addini musamman waɗanda suka gabatar da kwangilar Muslim-Muslim, manyan Arewa harma da talakawan, kowa yaja baki yayi shuru, sabida siyasa, sabida tsabar munafurci da rashin sanin kai. A yanzu duk wanda zai yi ƙorafi game da shigowar sojojin Isra’ila Najeriya, kallon ɗan adawar Tinubu da APC ake masa. Sai bayan Isra’ilar ta shigo ta soma illata mu kamar yadda suke yiwa Falatsinawa da ragowar ƙasashen Musulmai, sannan za’a tashi da ihu bayan hari, ace ayi ta addu’a. 

Rashin sanin kai, sakaci, watsi da kyawawan al’dun mu, ƙiyayyar juna kamar yadda Marigayi Malam Aminu Kano ya taba faɗi, da munafurci, sune manyan matsalolin dake damun ƴan Arewa a yanzu.

Abinda ya janyo mana hakan kuwa shine rashin haɗin kai, rarrabuwan kai a siyasa, rashin fahimtar addini, jahilci, da tarin al’uma da basa amafanar da juna. 

Matuƙar muna so muyi maganin matsalolin dake addabar yankin mu na Arewa, dole mu tashi tsaye wajen  bijiro da hanyoyin gyara al’amuran yankin mu. Hakan kuma bazai samu ba, sai mun haɗa kai mun nemo JAGORANCI nagari. #YanArewa #northernnigeria

Sufyan manazarci kuma mai sharhi kan harkokin yau da kullum ne a Nijeriya

By ukarofi