Gwamnatin Katsina ta jaddada goyon baya ga sojoji kan yadda suke yaƙi da ta’addanci

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.

Muƙaddashin gwamnan Jihar Katsina, Malam Faruok Lawal Joɓe ya bayyana hakan lokacin da ya karɓi babban hafsan sojojin ƙasa, Laftanar Janar O.O. Oluyemi, a fadar gwamnatin jihar.Ya yaba da ƙoƙari da sadaukar da kai da jami’an tsaro a jihar .

Muƙaddashin gwamnan wanda harwala yau shine mataimakin gwamnan jihar ya jaddada cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da neman haɗin kai daga rundunar sojojin ƙasa da kuma sojojin sama domin kawo ƙarshen matsalolin tsaro baki ɗaya.

Malam Farouk Joɓe ya ce daga tattaunawa da yayi da babban hafsan sojojin”Ina mai ƙwarin gwiwa cewa daga matsalar rashin tsaro a Katsina nan ba da jimawa ba zai zama tarihi,”Joɓe ya ce
Muƙaddashin gwamnan ya bayyana jin daɗin sa kan shirin rundunar sojojin Najeriya na kafa bataliya a yankin Funtua, domin taimakawa rundunar da ke Katsina da kuma Daura wajen tunkarar ƙalubalen tsaro.

Ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatin jihar wajen ci gaba da saka hannun jari a ɓangaren tsaro, da kuma ɗaukar mutane daga al’umma domin tallafawa jami’an tsaro.

Ya yi wa sojojin kira da su ƙarfafa kai hare-hare ta sama tare da ƙarin dakarun sojojin ƙasa musamman a yankunan da ake fama da matsalar ’yan ta’adda.

A nasa jawabin, babban hafsan sojojin ƙasa, Laftanar Janar O.O. Oluyemi,ya ce ziyararsa a Katsina wani ɓangare ne na rangadin aiki, tare da yin ta’aziyya ga al’ummar jihar bisa asarar rayuka da aka yi a harin ’yan ta’adda da ya faru kwanan nan a Gidan Mantau da ke ƙaramar hukumar Maluumfashi.

Janar Oluyemi ya gode wa gwamnatin Katsina bisa irin goyon bayan da take bai wa rundunar sojoji, tare da tabbatar da cewa rundunar ba za ta gajiya ba wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Ya kuma jaddada muhimmancin haɗa kai musamman a fannin rabawa da musayar bayanan sirri, domin hakan zai taimaka wa jami’an tsaro wajen fatattakar ‘yan ta’adda da tabbatar da ɗorewar zaman lafiya a jihar.

Wannan ziyara da janar Oluyemi ya kawo jihar bai rasa nasaba da mummunan hari da ƴan bindiga suka kai a wani masallaci da ke Gidan Mantau inda suka kashe mutane fiye da 50.

Koda yake daga baya kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro ya tabbatar da cewa mutane 28 ne suka mutu saka makon hare haren.

By ukarofi