‘Yan bindiga sun yi awon gaba da magidanci da iyalansa a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wasu mutane ɗauke da makamai da ake zargin ɓarayin daji ne sun kutsa kai cikin birnin Katsina, inda suka sace wani magidanci mai suna Anas Ahmed tare da mai ɗakinsa Halimatu da kuma ‘yarsu.

Wani mazaunin unguwar da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaidawa Blueprint Manhaja cewa, lamarin ya faru a Sabuwar Unguwa, Filin Kanada da misalin ƙarfe 3:00 na dare.

Maharan sun Kuma hallaka wani ɗan banga dake aikin samar da tsaro a yankin.

Yanzu haka dai lamarin ya saka mazauna unguwar cikin tsoro da fargaba duba da cewa ba a fiye samun rahotannin shigar masu garkuwa da mutane cikin babban birnin Jihar ba.

Kawo yanzu rundunar ‘yan sandan Katsina ba ta yi ƙarin haske ba game da faruwar lamarin.

By ukarofi