Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ƙungiyar ‘yan kasuwa, masana’antu, ma’adinai da noma ta jihar Zamfara, ZACCIMA, ta ƙaryata raɗe-raɗin da ake ta yaɗuwa a shafukan sada zumunta na cewa Gwamna Dauda Lawal ya soke rancen da gwamnatin jihar ta yi alƙawarin bai wa mambobin ta da su kayi majalisa da ita.
Shugaban ZACCIMA na jihar Dr. Hassan Buhari ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Gusau.
Dokta Hassan ya bayyana raɗe-raɗin da ake yi kan lamarin a matsayin ƙarya tsagwaron ta da kuma mugun nufi ga masu raɗe raɗin ga ƙungiyar.
A cewarsa, raɗe raɗin na da alaƙa da siyasa.
Ya ce masu wannan hasashe suna yine don cimma manufar su wajen ganin shirin bai cimma nasara ba.
A cewar sa, gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar bankin masana’antu sun amince da karɓar lamunin ga ƙananan ’yan kasuwa da matsakaita da kuma manya a jihar da nufin bunƙasa sana’o’insu.
Ya bayyana cewar ƙungiyoyin ‘yan kasuwa sama da 2000 ne aka yi wa rajista domin cin gajiyar shirin rancen, inda ya ce an riga an shirya duk wani shiri na fitar da rancen nan ba da daɗewa ba.
Dokta Hassan Buhari ya ci gaba da bayyana cewa ƙungiyar ta gabatar da sama da ƙudurin ta ga gwamnatin jihar na zunzurutun kuɗi Naira biliyan 20 domin gwamnatin jihar ta bada rancen don amfanin ‘yan kungiyar da suka yi rajista.
Ya kuma buƙaci mambobin ƙungiyar da su yi watsi da raɗe raɗin da ake yi na janye shirin ba da lamunin da gwamnatin jihar tayi alƙawari, inda ya ce ƙungiyar ƙarƙashin shugabancin sa na aiki ba dare ba rana domin ganin tabbatuwar shirin.
