Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‘Yan bindigan da suka sace magidanci a Katsina mai suna Anas Ahmad da iyalan sa sun tuntuɓi ƴan uwansa inda suka nemi a basu kuɗin fansa Naira miliyan 600 kafin su sake su.
Mazauna unguwar sun shaida cewa Anas Ahmad matashin ɗan kasuwa ne mai taimakawa al’umma ga shi da son mutane.
Tun ranar da lamarin ya faru kwamishinan ƴan sanda CP Bello Shehu tare da manyan jami’an sa suka isa gidan Anas domin gane ma idanunsa.
Kwamishinan ya bada umurnin baza jami’an ƴan sanda ciki da wajen Katsina don gano tare da kama waɗanda suka aikata wannan ta’addanci.
Maharan sun shiga Unguwar Kanada da ke cikin garin Katsina suka sace magidancin Anas Ahmad da matarsa Halimatu wanda ke ɗauke da juna biyu da ɗiyar sa.
Harin na yan bindigan yayi sanadiyyar mutuwar wani ɗan banga da yake aikin bada tsaro a yankin.
