
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta tsare Sirajo Salisu Usman, wanda ɗan uwa ne na Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman (wanda aka fi sani da Pakistan) bisa zarginsa da hannu a badaƙalar biliyoyin nairori.
A ranar Laraba jami’an EFCC suka kama shi a Abuja.
Tun a farkon watan nan na Agusta ne aka yi wani bincike akansa da kuma wasu jami’an NAHCON akan ɓatar kuɗaɗen.
Majiyoyi daga EFCC sun shaida cewa, Usman, wanda ake kira da ‘ka fi ciyaman’, ma’ana shugaban tsagi na NAHCON, ya kwana ne a ofishin EFCC a Abuja a ranar Laraba.
Haka kuma, Sirajo Usman, wanda ɗan gida ɗaya ne da Farfesa Pakistan, shi ne mataimakin darakta a ofishin Shugaban na NAHCON.
Majiyoyin sun shaida cewa ana gudanar da bincike ne akansa bisa hannu a ɓatar sama da Naira biliyan 50 na dukiyar al’umma.
Rahotanni sun bayyana cewa, a aikin hajjin 2025 kaɗai, an yi zargin NAHCON ta ɓarnatar da kimanin biliyan N25 a masaukin Masha’ir da ƙarin wasu biliyan N9.6 a wasu kashe-kashe.
