Na ɗauki alhakin hatsarin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna – Shugaban NRC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC), Kayode Opeifa, ya ce ya ɗauki alhakin hatsarin jirgin ƙasa da aka samu ranar Talata, wanda aka samu lokacin da jirgin ya kama hanya daga Abuja babban birnin ƙasar zuwa Kaduna.

A tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, Opeifa ya ce ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen binciken abin da ya sanya jirgin ya kauce daga kan layi.

“Bayan neman gafarar ‘yan Nijeriya, a matsayina na shugaban hukumar, na ɗauki cikakken alhakin abin da ya faru,” inji shi.

Opeifa ya tabbatar da cewa duk da cewa hatsarin bai kamata ya faru ba, NRC za ta tabbatar hakan bai sake faruwa ba.

Hatsarin ya faru ne a ranar Talata bayan jirgin ya tashi daga Abuja da misalin ƙarfe 11 na safe kan hanyar zuwa Kaduna da ke arewacin Nijeriya, lamarin da ya jefa fasinjoji cikin da ruɗani da tsoro.

Hukumar agajin gaggawa ta Nijeriya ta ce hatsarin ya jikkata mutum bakwai, waɗanda suka samu kulawar malaman lafiya.

Jirgin ƙasa  Abuja zuwa Kaduna ya yi ƙaurin suna kan samu tangarɗa a kai a kai.

A bara jirgin ya samu tangarɗa a kusa da garin Jere, sai dai babu wani fasinja da ya jikkata, haka nan ma an samu irin haka a 2023 a kusa da tashar jirgin ƙasa ta Kubwa.

Tangarda mafi muni da jirgin ya samu a tarihinsa shi ne lokacin da aka tsayar da ayyukansa na tsawon wata shida a shekara ta 2022 bayan da wasu gungun yan bindiga suka kai masa farmaki tare da yin garkuwa da kimanin mutum 60.

A shekara ta 2016 ne aka ƙaddamar da sufurin jirgin ƙasan daga Abuja zuwa Kaduna mai nisan kilomita 186 domin samar wa matafiya zaɓi daga bin hanyar mota, lokacin da ake fama da matsalar tsaro ta ‘yan bindiga masu tare hanya suna garkuwa da mutane.

By ukarofi