Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), reshen Jihar Kaduna, ta yaba wa Gwamna Uba Sani bisa dawo da wasu daga cikin malaman makaranta da gwamnatin Nasir El-Rufa’i ta kora a jihar.
Shugaban NLC na Jihar Kaduna, Ayuba Suleiman ne ya yi wannan yabo yayin da ya ke jawabi ga mambobin ƙungiyar ‘Yan Jaridu Masu Bincike ta ƙasa (NGIJ) wadanda ke jihar domin duba yadda ake tafiyar da mulki.
A tuna cewa gwamnatin da ta gabata Kaduna karkashin Nasir El-Rufai ta kori malamai sama da dubu 23, ciki har da tsohon Shugaban Kungiyar Malaman Makaranta ta Kasa (NUT), tsakanin shekarar 2018 zuwa 2021.
Suleiman ya bayyana cewa gwamnatin Kaduna mai ci ta dawo da shugabannin makarantu, ma’aikatan gudanarwa da malamai na koyar da kimiyya da abin ya shafa, yana mai cewa ana ci gaba da gyara kura-kuran da gwamnatin baya ta tafka.
