Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Zuwa yanzu ƙananan hukumomi biyar kenan su kayi sasanci da yan bindiga a yankunan su da ke jihar.
Sun haɗa da ƙananan hukumomin Jibiya, Batsari, Ɗanmusa, Safana da na baya bayan nan kurfi.
Maradin Katsina hakimin Kurfi Alhaji Mansur Amadu Kurfi da shugaban ƙaramar hukumar Kurfi Hon. Babangida Abdullahi Kurfi su ka jagoranci sasanci da ‘yan bindiga da su ka addabi ƙaramar hukumar domin maslaha da zaman lafiyar al’ummar yankin.
Ƙaramar hukumar kurfi na ɗaya daga cikin yankin da su kai fama da aikace-aikacen yan ta’adda a yankin.
A jawabin sa wajen taron, Maradin Katsina hakimin Kurfi Alhaji Mansur Amadu Kurfi ya nuna jin daɗin shi akan wannan sasanci da a kayi domin maslahar al’umma, ya kuma yi alƙawarin riƙe amana ta Fulanin dajin.
Hakimin ya kuma umurci shugabannin su kawo wasu daga cikinsu a naɗa su shugabannin su na gargajiya.
Shugabannin Fulanin Dajin da suka jagoranci ɓangaren su wajen taron sasancin sun haɗa da Alhaji Usman Kachalla Ruga, Sani Muhindinge, Yahaya Sani (Hayyu), da Alhaji Shu’aibu.
Shugabannin sun bayyana cikakken goyon bayansu akan wannan sasanci da a kayi tare da ɗaukar alƙawarin daina kai hare, hare, da kashe, kashe, da satar mutane don neman kudin fansa, gami da satar shanu, a yankin ƙaramar hukumar Kurfi.
Sun kuma sharwaci manoman yankin su ci gaba da harkokin nomansu cikin walwala ba tare da wata fargaba ba.
Sai suka yi kira da a sako masu mutanen su dake tsare, kuma suma za suje su sako mutanen dake wurinsu bada wata jinkiri ba domin kowa ya koma gidanshi, “zaman lafiya ya samu a ƙaramar hukumar Kurfi babu sauran wani tashin hankali sun ɗauki alƙawari,”inji tubabbun yan bindigan.
A nasa jawabin, shugaban ƙaramar hukumar Kurfi Hon. Babangida Abdullahi Kurfi ya bayyana farin cikinsa na kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙaramar hukumar Kurfi, sannan ya yi alƙawarin cika duk buƙatun da Fulanin Dajin su ka nema.
Tun daga gyara masu makarantu, asibitoci, da kuma binciken mutanen su dake tsare tare da sako su, su koma cikin yan uwansu da iyalansu.
Shugaban ƙaramar hukumar ya bada umurni bayan kammala wannan zaman sasanci, Fulani Dajin za su iya shiga ko ina a cikin ƙaramar hukumar su gudanar da harkokin su cikin walwala ba tare da tsangwama ba.
Taron da aka gudanar a dajin Wurma dake cikin ƙaramar hukumar Kurfi ya samu halartar iyayen ƙasa, mutanen gari na yankunan da suke fama da wannan matsala.
Ana ta samu mabanbantan ra’ayi dangane da sasanci tsakanin ƴan bindiga da wasu ƙananan hukumomin da ke jihar.
Gwamna Dikko Raɗɗa yasha nanata cewa gwamnatin sa ba za ta yi sasanci da ‘yan bindiga ba amma idan su suka buƙaci ayi zaman sasancin ta a shirye yake ya tattaunawa da su.
