Sakkwato: A wani karo, da dama sun rasu a kifewar kwale-kwale

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani hatsarin kwale-kwale da ke maƙare mutane da kayayyaki a yammacin ranar Alhamis ya yi sanadin rasuwar fasinjoji da dama a Ƙaramar Hukumar Shagari da ke Jihar Sakkwato.

Mai taimaka wa Gwamna Ahmed Aliyu akan lamuran gaggawa, Aminu Bodinga ya tabbatar wa manema labarai hakan a yau Juma’a inda ya ce an aika da jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta jihar (SEMA) zuwa wajen da abin ya faru.

Ya ce, hatsarin ya auku ne da wani gajiyayyen kwale-kwale a lokacin da ya ɗebo fasinjoji masu yawa tare da kifar da su baki ɗaya.

Ya kuma ce, kawo yanzu ba a san adadin waɗanda iftila’in ya rutsa da su ba, inda ake tunanin da dama daga cikinsu ba su tsira ba.

Wannan shi ne karo na biyu a wannan makon inda wani kwale-kwale da ke ɗauke da mutane sama da 50 da galibinsu manoma da ƙananan ƴan kasuwa ne suka nutse a wani kogi ranar Lahadi.

Rahotanni sun bayyana cewa, an yi nasarar ceto mutane 25 a raye yayin da aka samo gawawaki guda uku a yayin bincike.

By Babaji